Kungiyar Daliban Najeriya ta Kasa
Kungiyar Dalibai ta Kasa (NUNS) kungiya ce ta dalibai da ta haɗa daliban Najeriya a cikin Najeriya da kuma ƙasashen waje.
National Association of Nigerian Students | |
---|---|
students' union (en) | |
Bayanai | |
Farawa | 1956 |
Ƙasa | Najeriya |
Tarihi
gyara sasheAn kafa kungiyar NUNS a cikin shekarar 1956, bayan sauye-sauyen tsari a cikin Ƙungiyar Dalibai ta Yammacin Afirka. Ƙungiyar ta haɗa majalisar dalibai a Ife, Zaria, da Nsukka.[1]
A cikin watan Afrilun 1978, ɗaliban Najeriya sun fuskanci ƙarin kuɗaɗen makarantu, kuma haɗaɗɗiyar kungiyar NUNS da ta haɗa da jami'o'i a faɗin ƙasar sun halarci zanga-zangar; Ali Must Go. Gwamnati ta mayar da martani ta hanyar tura sojoji da 'yan sanda, lamarin da ya yi sanadin mutuwar dalibai sama da ashirin ko kuma suka samu munanan raunuka. An rufe jami'o'i uku kuma an dakatar da NUNS. An sallami wasu ma’aikatan Jami’a da dalibai da dama.[2]
Kowane shugaban ƙungiyar yana da wa'adin shekara 1 kuma shugaban da aka zaba a ranar 4 ga Satumba shi ne Umar Faruq Lawal.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "National Union of Nigerian Students (NUNS)". Facts On File. Retrieved 13 December 2013.
- ↑ Coutsoukis, Photius. "Nigeria Student Organizations". Archived from the original on 12 September 2015. Retrieved 13 December 2013.
- ↑ "Nans presidential election". Vanguard news.