Kole Ade-Odutola mawaƙin ƙabilarYarbawa kuma ɗan Najeriya ne, mai daukar hoto, haka zalika Malami. [1] [2] Ya wallafa litattafai da dama na waƙoƙi, ciki har da The Poet Bled da The Poet Fled . Ya kasance mai mahimmanci a lokacin assasa Coalition of Nigerian Artists (CONA), wanda ke bayar da shawara ga gwamnatin Najeriya don ingantaccen hangen nesa a fannin Fasaha. [3] Ya halarci taruka daban-daban domin neman yancin walwala da samun dama ga Fasaha da ma, tofa albarkacin baki a Najeriya. [3] [4]

Kole Ade-Odutola
Rayuwa
Karatu
Makaranta Jami'ar jahar Benin 1984) Digiri a kimiyya : Botany
University of Reading (en) Fassara 1998) master's degree (en) Fassara
Rutgers University (en) Fassara 2010) Doctor of Philosophy (en) Fassara : media studies (en) Fassara
Ithaca College (en) Fassara 2000) master's degree (en) Fassara : organizational communication (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a marubuci da maiwaƙe
Employers University of Florida (en) Fassara

Odutola ya sami digiri na farko na Kimiyya a fannin Botany a shekarar 1984 daga Jami'ar Benin, a 1998, Digiri na biyu a fannin TV/Video daga Jami'ar University of Reading Ya kuma yin karatun digiri na biyu a fannin Organizational Communication, Learning & Design (OCLD) a Kwalejin Ithaca. Ya kammala a shekarar 2000. Daga baya ya shiga Makarantar Sadarwa, Watsa Labarai da Kimiyyar Laburare ta Jami'ar Rutgers, inda ya sami digirin girmamawa na Falsafa a fannin Nazarin Watsa Labarai a shekarar 2010. [5] [6] Ya yi aiki a matsayin malami a Jami'ar Rutgers [7] a halin yanzu yana koyar da harshe da al'adu a Jami'ar Florida, wanda ya soma tun a shekara ta 2006. [5] [8] [9]

Odutola ya gabatar da jawabai daban-daban, laccoci, da gabatarwa a fannin Nollywood, adabi da wakoki da kafafen yada labarai a Najeriya a wasu taruka cikin gida Najeriya da ma tarukan ƙasashe. [10] [11] [12]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Hurray, Osadolor is 60". The Guardian Nigeria (in Turanci). 2020-08-15. Retrieved 2021-10-01.
  2. "Poetry by Kole Ade Odutola". The New Black Magazine. Retrieved 2021-10-01.
  3. 3.0 3.1 "Re-inventing arts, culture administration in post COVID-19 lockdown era". The Guardian Nigeria (in Turanci). 2020-08-30. Retrieved 2021-10-01.
  4. "Academics, lawyers, journalists demand Sowore's release". Premium Times (in Turanci). 2019-11-10. Retrieved 2021-10-01.
  5. 5.0 5.1 "Kole Ade Odutola". University of Florida (in Turanci). Retrieved 2021-10-01.
  6. "Kole Odutola | University of Florida". Academia. Retrieved 2021-10-01.
  7. "Ajiba-date, By Kole Ade-Odutola - Premium Times Opinion". Premium Times (in Turanci). 2018-05-28. Retrieved 2021-10-01.
  8. "Kole Odutola". Google Scholar. Retrieved 2021-10-01.
  9. Syed, Camille. "FDOT addresses safety after University of Florida football player dragged by semi truck". WCJB Gainesville (in Turanci). Retrieved 2021-10-01.
  10. "New Year, new conversations around Nollywood". The Guardian Nigeria (in Turanci). 2020-01-12. Retrieved 2021-10-01.
  11. "TRIBUTE: Oronto Douglas' private views about Nigerian journalism, nationhood... Nollywood". TheCable (in Turanci). 2015-04-10. Retrieved 2021-10-01.
  12. "Nigeria Prize for Literature Parties with Past Winners". This Day Live (in Turanci). 2020-10-18. Retrieved 2021-10-01.