Kiumeni (Eng: Masculinity), fim ne na ban dariya na shekarar 2017 na Tanzaniya wanda Nicholas Marwa ya ba da umarni kuma Daniel Manege da Ernest Napoleon suka shirya ga D-Magic da Busy Bees. Taurarin shirin sun haɗa da Antu Mendoza da Ernest Napoleon a matsayin jagorori tare da Irene Paul, Idris Sultan da Akbar Thabeet.[1] Fim ɗin kacokan na magana akan labarin soyayya ne na Swahili tsakanin duniyoyi guda biyu tare; wani mawadaci ya haɗu da budurwarsa a unguwar ta marasa kudi sosai.[2]

Kiumeni
Asali
Ƙasar asali Tanzaniya
Characteristics
External links

Fim ɗin ya sami yabo sosai kuma an zaɓi shi a hukumance don nunawa a bukukuwan fina-finai na duniya da yawa. Fim din ya lashe kyautar mafi kyawun wasan kwaikwayo da kuma mafi kyawun bayar da umarni a bikin fina-finai na Zanzibar na kasa da kasa na 2017. An shirya fim ɗin a birnin Dar es Salaam kuma an yi fim a ciki da kewayen biranen: Mikocheni, Kinondoni, Sinza, Mbezi, Mwananyamala da Mburahati.

Yan wasan shirin

gyara sashe
  • Antu Mendoza a matsayin Faith
  • Ernest Napoleon a matsayin Gue
  • Irene Paul a matsayin Irene
  • Idris Sultan a matsayin Gasper
  • Akbar Thabeet a matsayin Masti

Manazarta

gyara sashe
  1. "Tanzanian film Kiumeni takes on the bongo film industry". Screen Africa. 15 March 2018. Retrieved 31 October 2020.
  2. "'Kiumeni' the next hit in Bongo movies". thecitizen. Retrieved 31 October 2020.

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe