Kisan kiyashi a Jihar Plateau, 2022
A ranar 10 ga Afrilu, 2022, wasu gungun ‘yan bindiga sun kashe mutane sama da 150 a wasu jerin hare-hare a jihar Filato, Najeriya. Hare-haren na da nasaba da rikicin ‘yan bindiga da ake ci gaba da yi a Najeriya. An kuma yi garkuwa da mutane kusan 70 a hare-haren.[1]
| ||||
Iri |
harin ta'addanci mass shooting (en) Garkuwa da Mutane | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 10 ga Afirilu, 2022 | |||
Wuri |
Kanam Wase Chikun | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 150 | |||
Perpetrator (en) | mai-ta'adi |
Bayan fage
gyara sasheNajeriya na fama da munanan tashe -tashen hankula da dama. Wadannan sun haɗa da rikicin Boko Haram, wanda ya fara a shekarar 2009, da kuma rikicin ‘yan bindigan Najeriya, wanda ya faro a shekarar 2011.[2]
A farkon 2020s, hare-haren 'yan fashi sun ƙaru. Mako guda kafin harin, ‘yan bindiga sun kai wani gagarumin hari a sansanin soji a jihar Kaduna, inda suka kashe sojoji 15.[3] Wani hari da aka kai kan bikin girbi a wancan makon ya kashe mutane 17.[4] Makonni kaɗan da suka wuce, wani hari da aka kai kan wani jirgin kasa da ke kan hanyarsa ta zuwa Kaduna, ya halaka fasinjoji sama da 60.[5]
A ranar da aka kai harin, ‘yan bindiga sun kashe mutane 15 a wani lamari da ba ya da alaka da shi. Kisan kiyashin ya faru ne a wani ƙauye da ke Chikun a jihar Kaduna. Shugaban al’ummar yankin Isiaku Madaki wanda aka naɗa kasa da kwana guda yana cikin waɗanda suka mutu.[6]
Harin
gyara sasheA ranar 10 ga Afrilu, 2022, wasu gungun ‘yan bindiga, waɗanda ake kyautata zaton Fulani makiyaya ne[7] sun kai hari a kauyuka tara a jihar Filato.[8][3] Dukkan ƙauyukan suna cikin kananan hukumomin Kanam da Wase.[9] ‘Yan bindiga sun kashe akalla mutane 50 tare da yin garkuwa da wasu kusan 70.[8] [3] Haka kuma sun kona gidaje da wawushe dukiyoyi a lokacin da suka yi tashe-tashen hankula. [8] [3]
An binne waɗanda suka mutu a hare-haren a cikin kaburbura a garin Kanam.[9]
Martani
gyara sasheYayin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa "ba za a yi rahama" ga waɗanda suka kai wadannan hare-hare ba, shugabannin al'ummomin yankin sun yi kira da ya yi murabus saboda gazawarsa wajen tabbatar da tsaro.[1]
Abubuwan da suka faru
gyara sasheRahotannin farko na hukumomi sun ce an kashe akalla mutane 50. Shaidu sun shaida wa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa adadin waɗanda suka mutu ya zarce 100, yayin da wasu kuma suka ce akalla mutane 130.[7] A ranar 11 ga Afrilu, Muryar Amurka ta ce an kashe akalla mutane 70.[4] Jaridar Vanguard ta ruwaito an kashe akalla mutane 78 a Kanam da kuma wasu 15 a Chikun yayin hare-haren.[6]
Duba kuma
gyara sashe- Jerin kisan kiyashi a Najeriya
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 Carter, Sarah. "Nigeria leader vows "no mercy" for gunmen behind massacre that left more than 150 dead in country's north". CBS.
- ↑ "Peace talks bring fragile truce in Nigeria 'bandit' conflict". news.yahoo.com (in Turanci). Retrieved 2022-04-21.
- ↑ 3.0 3.1 3.2 3.3 Dzirutwe, MacDonald (11 April 2022). "Gunmen attack kills at least 50 in Nigeria's Plateau state". Reuters (in Turanci). Retrieved 12 April 2022.
- ↑ 4.0 4.1 Obiezu, Timothy. "Police Deploy to Villages in Nigeria's Plateau State After Attacks Kill 70". Voice of America (in Turanci). Retrieved 12 April 2022.
- ↑ Abe, Bankole (29 March 2022). "Train attack: Number of persons feared dead rises as Tinubu says 60 were killed". International Centre for Investigative Reporting (in Turanci). Retrieved 18 April 2022.
- ↑ 6.0 6.1 Nanlong, Marie-Therese; Hassan-Wuyo, Ibrahim; Abubakar, Shina (12 April 2022). "94 killed by terrorists, assassins in Plateau, Kaduna, Osun within 24 hrs". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 12 April 2022.
- ↑ 7.0 7.1 Asadu, Chinedu (12 April 2022). "Gunmen kill more than 100 in Nigeria's north, say survivors". Associated Press (in Turanci). Retrieved 12 April 2022.
- ↑ 8.0 8.1 8.2 "Nigeria: Gunmen attack kills at least 50 in Plateau state". Al Jazeera (in Turanci). 12 April 2022. Retrieved 12 April 2022.
- ↑ 9.0 9.1 "Victims Of Plateau Attacks Buried In Mass Grave". Channels Television. 12 April 2022. Retrieved 12 April 2022.