Khemaies Jhinaoui, (an haife shi a ranar 5 ga watan, Afrilu a shikara ta 1954) wani jami’in diflomasiyyar Tunusiya ne wanda ya yi aiki a matsayin Ministan Harkokin Wajen Tunisia daga shekarar 2016 zuwa 2019. [1] Jhinaoui ya taba zama Jakadan Rasha da Ukraine daga Disamba 2001 zuwa Yunin shekarata 2011.

Khemaies Jhinaoui
Minister of Foreign Affairs (en) Fassara

6 ga Janairu, 2016 - 29 Oktoba 2019
Taïeb Baccouche (en) Fassara - Sabri Bachtobji (en) Fassara
Rayuwa
Haihuwa Kairouan (en) Fassara, 5 ga Afirilu, 1954 (70 shekaru)
ƙasa French protectorate of Tunisia (en) Fassara
Tunisiya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai wanzar da zaman lafiya da Lauya
Imani
Jam'iyar siyasa independent politician (en) Fassara
Call for Tunisia (en) Fassara


Tarihi da karatu

gyara sashe

Khemaies Jhinaoui ta sami digiri nafarko a shari'ar jama'a, da digiri na biyu a dokar jama'a da kuma takardar shaidar karatun ci gaba a fannin kimiyyar siyasa da alakar kasashen duniya. A shekarar 1978, ya sami takardar shedar kwarewa a aikin lauya.

 
Khemaies Jhinaoui a zaune a gefe

A shekarata 1979, Jhinaoui ya fara aiki a Ma'aikatar Harkokin Wajen, inda ya rike mukamai da yawa a cikin jami'an diflomasiyya.

 
Khemaies Jhinaoui suna gaisawa

A watan Mayu na shekarar 1996, an tura shi zuwa Isra’ila domin ya bude ofishin kula da sha’awar kasarsa a Tel Aviv . [2] A watan Janairun 2006, an nada shi darektan harkokin siyasa da tattalin arziki da hadin gwiwa tare da Turai da Tarayyar Turai a ma'aikatar harkokin waje.

Girmamawa

gyara sashe
  • 2011 : Kwamandan Umurnin Jamhuriyar Tunisia
  • 2019 : Babban Jami'in Umurnin Jamhuriyar Tunisia
  • 2019 : Memba na girmamawa na Xirka Ġieħ ir-Repubblika na Malta

Duba kuma

gyara sashe
  • Jerin sunayen ministocin harkokin waje a shekarar 2017
  • Jerin sunayen ministocin harkokin waje na yanzu

Manazarta

gyara sashe

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe
  1. "Tunisia PM in sweeping cabinet reshuffle", Agence France-Presse, 6 January 2016.
  2. Family in the Middle East: Ideational Change in Egypt, Iran, and Tunisia