Khalida Zahir (Larabci: خالدة زاهر‎; 1927–2015, wanda kuma aka rubuta Khalda Zahir), ta kasance ɗaya daga cikin likitocin Sudan mata na farko kuma mai fafutukar kare hakkin mata.

Khalida Zahir
Rayuwa
Haihuwa Omdurman, 18 ga Janairu, 1927
ƙasa Sudan
Mutuwa 9 ga Yuni, 2015
Karatu
Makaranta Faculty of Medicine University of Khartoum (en) Fassara
Sana'a
Sana'a likita da Mai kare hakkin mata
Mamba Kungiyar matan sudan

Ƙuruciya da ilimi

gyara sashe

An haifi Zahir a Omdurman. Ta kammala karatu daga Makarantar Magunguna ta Kitchener, wacce daga baya ta zama Jami'ar Khartoum, a shekara ta 1952, tare da Z Serkisiani.[1]

Aikin likita

gyara sashe

Khalida da Serkisiani su ne likitoci mata na farko a Sudan.[1]

 
Khalida Zahir

Khalida ta yi wa talakawa kyauta a asibitinta. Ta zama shugabar kula da lafiyar yara a ma'aikatar lafiya ta Sudan. Ta yi ritaya a shekarar 1986.[2]

Harkar siyasa

gyara sashe

Khalida ita ce mace ta farko a cikin kungiyar ɗalibai a shekarar 1947 kuma ta shiga tattaunawar zaman lafiya dangane da kudancin Sudan a wannan shekarar. Khalida ta kasance ɗaya daga cikin mata kalilan da suka shiga jam’iyyar siyasa a shekarun 1940. Ta kafa kungiyar al'adu ta matasa tare da Fatima Talib a shekara ta 1948.[3] Kungiyar mata ta Sudan ta farko, ta ba da ilimi ga mata kan kiwon lafiya, karatu da rubutu.[2] Ta kasance cikin waɗanda suka kafa kungiyar mata ta Sudan (SWU) a shekarar 1952, kungiyar da ta yi fafutukar neman zaɓe da yancin aiki.[2] An zaɓi Khalida shugabar SWU a shekarar 1958.[4]

Khalida ta rasu ranar 9 ga watan Yuni 2015.[4]

Manazarta

gyara sashe
  1. 1.0 1.1 Mohamed IN, Abdelraheem MB, Abdullah MA (2012). "Sudanese female doctors in paediatrics" (PDF). Sudanese Journal of Paediatrics. 12 (2): 36–43. PMC 4949896. PMID 27493343.
  2. 2.0 2.1 2.2 Mubarak, Khalid Al (2015-06-23). "Khalida Zahir obituary". The Guardian (in Turanci). ISSN 0261-3077. Retrieved 2016-11-20.
  3. Turshen, Meredeth (2000-01-01). African Women's Health (in Turanci). Africa World Press. pp. xi. ISBN 9780865438125 – via Google Books.
  4. 4.0 4.1 Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named Sudanow_women_role_indep