Kasuwar Dawanau
Kasuwar Dawanau Ita ce kasuwar hatsi mafi girma a Nahiyar Afirka, saboda da girma na hada-hadar kasuwanci da ya ke faruwa a cikin kasuwar a kullum.Tana cikin garin Dawanau dake Karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano, Najeriya.
Kasuwar Dawanau | ||||
---|---|---|---|---|
kasuwa | ||||
Bayanai | ||||
Ƙasa | Najeriya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | jihar Kano |
Tarihi
gyara sasheKasuwar Dawanau tsohuwar kasuwar hatsi ce a Najeriya da Afirka.Tana cikin garin Dawanau, karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Ayyuka
gyara sasheKasuwar Dawanau ta kasance kasuwar hatsi mafi girma a Afirka. Tana tattara masu saye da sayarwa daga kasashe daban-daban na Afirka, Turai, Asiya, Amurka da Saudia. Ana kuma safarar kayayyaki a kowace rana zuwa Togo, Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Nijar, Ghana tsakiyar Afirka, Afirka ta Kudu, libya da sauran kasashen Afirka. A wajen Afirka, yan kasuwa daga Burma, Dubai, India, China, Burtaniya, Saudi Arabia, America da sauran kasashe suma suna tallafawa kasuwar hatsi don abubuwa kamar su zogale da ganyaye, iri essame, furen Hibuscus (Sobu) da sauran abubuwa kamar suya wake, Wake, Rogo, Gero, masarar Guinea, da sauran abubuwa. [1]
Manazarta
gyara sashe.