Kamfanin Inshora na Allianz
Kamfanin Allianz Nigeria Insurance Ltd (wanda a da ake kira da Ensure Insurance plc ) ya kasance kamfani ne mai zaman kansa a Najeriya. Hukumar Inshora ta ƙasa ce ta ba ta lasisi, wadda ita ce muhimmiyar hukumar inshorar a kasar Najeriya.[ana buƙatar hujja]
Bayanai
gyara sasheAllianz na bada hidiman inshora na rayuwa da na dukiya waɗanda suka haɗa da ababen hawa, gida, inshorar rayuwa da ilimi gami da tsare-tsaren ajiya.
Har ila yau, kamfanin yana sayar da ire-iren inshora na kasuwanci, ciki har da wuta da haɗari na musamman, ɓarna, hadari na kayan kwamfuta da kayan lantarki, kuɗi, tilastawa, rasa aiki, haɗari na injina / shuka, ƴan kwangila / haɓakawa, da kayayyaki-a cikin hanyar wucewa. inshora.[1]
Ana iya tuntuɓar Inshorar Allianz a wurare kamar haka
- Babban ofishin - Lagos Island
- Ikeja Office – Ikeja, Lagos
- Yaba Office - Yaba, Lagos
- Ofishin Festac - Garin Festac, Legas
- Abuja Office - Abuja
- Ofishin Port Harcourt – Fatakwal
- Ofishin Ibadan - Ibadan
- Benin Office - Benin City
Tarihi
gyara sasheAn ƙirƙiri kamfanin a cikin 1993 da farko a matsayin Kamfanin Assurance Company plc, an sake buɗe kamfanin a matsayin Ensure Insurance plc a shekara ta 2016. Allianz[2] suka siya kamfanin a cikin shekara ta 2018 kuma ya sake masa suna Allianz Nigeria Insurance plc. A cikin shekara ta 2017 ne, kamfanin ya samar da manyan kudaden da aka shigar N7.67billion wanda ke wakiltar cigaban na kaso 86% akan na shekara ta 2016 (N4.19billion). A watan Mayu 2018, Allianz Nigeria Insurance plc a hukumance ya zama kamfani na The Allianz Group. A watan Disamba na shekarar 2020, bisa dabarar sa, an kammala mayar da hannun jarin kamfanin gaba daya, kuma Allianz Nigeria Insurance plc ya daina aiki a matsayin kamfani na kasuwanci. Daga yanzu zai ci gaba da aiki a matsayin Allianz Nigeria Insurance Ltd.
Shugabanci
gyara sasheAllianz yana karkashin jagorancin kwamitin gudanarwa na mutsne shida. Dickie Ulu, shi ne jagorar majalisar. Adeolu Adewumi-Zer, Babban Darekta.[3]