Kamfanin Arnergy
Kamfanin Arnergy Solar Limited kamfani ne na samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana da ke birnin Legas, Najeriya.[1][2] Yana samar da mafita na samar da wutai mai amfani da hasken rana ga masu kananan sana'o'i a Najeriya.[3][4]
Kamfanin Arnergy | |
---|---|
kamfani | |
Bayanai | |
Masana'anta | solar power (en) |
Femi Adeyemo wanda kuma shi ne babban jami’in gudanarwa na kamfanin ne ya kafa kamfanin a shekara ta 2013.[5]
Arnergy sun sanya wuta mai karfi 3MW na wutar lantarki mai amfani da hasken rana da kuma fiye da 9MWh na iya ajiya a Najeriya.[6][7]
Tarihi
gyara sasheFemi Adeyemo ne ya kafa kamfanin a shekara ta 2013 daga kudin da ya tara daga aljihunsa.[8]
A cikin watan Yulin 2015, Bankin Masana'antu na Najeriya ya saka hannun jari a kamfanin don samarwa al'ummomin karkara wuta mai amfani da hasken rana.[9] Hukumar raya kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya UNDP ce ta tallafa wa aikin.[10] Daga baya, a cikin watan Disamba na 2015, Shirin Solar Nigeria, wani bangare na Sashen Ci Gaban Duniya (DfID), ya ba da fam 100,000 (US $ 146,000) don fadada ayyukanta Arewacin Najeriya.[11]
A watan Yuni 2019, Breakthrough Energy Ventures tare da Norfund sun sanya hannun jari na dala miliyan 9 a kamfanin.[7][12][13]
A watan Disamban 2020, Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ba da dala miliyan 9 don samar da wutan sola ga ’yan kasuwa 20, kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a yankunan karkara a kasar.[14]
A watan Fabrairun 2021, Babban Kwamishinan Canada ya jinjina wa kamfanin saboda kokarin da suke yi na inganta wuta a Najeriya. A cikin wannan shekarar, a watan Maris, kamfanin ta samu lambar yabo ta Africa Brand Award saboda gudunmawar da ta bayar wajen bunkasa wuta mai amfani da hasken rana a Najeriya.[15]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kazeem, Yomi (21 June 2016). "A pay-as-you-go solar solution could kickstart renewable energy adoption in Nigeria". Quartz.
- ↑ Idris, Abubakar (21 August 2016). "Africa taking giant strides to fix its electricity challenges". TechCabal.
- ↑ Rathi, Akshat (28 August 2019). "Bill Gates-led $1 billion fund expands its portfolio of startups fighting climate change". Quartz.
- ↑ Eleanya, Frank (27 June 2019). "How Arnergy's tech powered solution could dent Nigeria's energy poverty". Business Day (Nigeria).
- ↑ Mbele, Lerato (16 August 2019). "Could solar power end Nigeria's power cuts?". BBC News.
- ↑ Anaesoronye, Modestus (27 April 2021). "Nigeria's Arnergy makes Bill Gates top list of global renewable energy drivers". Business Day (Nigeria).
- ↑ 7.0 7.1 Akinpelu, Oluwadamilare (25 June 2019). "Nigerian Energy Startup Arnergy Seals $9m Funding, to Power 35,000 Businesses by 2023". TechNext.
- ↑ "Femi Adeyemo, CEO, Arnergy: Interview". Oxford Business Group. 8 November 2017. Archived from the original on 2020-12-01.
- ↑ Agunbiade, Tola (7 June 2016). "Arnergy is bringing pay-as-you-go solar power to rural communities across Nigeria". TechCabal.
- ↑ Fadoju, Lulu (20 July 2015). "Arnergy Secures Funding for its Renewable Energy program from Nigeria's BoI". TechCabal.
- ↑ Gbenga, Akinfenwa (5 June 2016). "Arnergy: Breaking fresh frontiers in renewable energy sector". The Guardian (Nigeria).
- ↑ "Nigerian renewable energy solutions provider Arnergy closes Series A financing" (Press release). Nigeria: The Guardian. 25 June 2019.
- ↑ "Nigeria's Arnergy raises $9mn for renewable energy". CNBC Africa. 28 June 2019.
- ↑ Godsgift, Onyedinefu (16 December 2020). "FG, Arnergy sign MoU, to deploy $9M for electrification of 20,000 businesses". Business Day (Nigeria).
- ↑ Anaesoronye, Modestus (2 February 2021). "Arnergy gets Canada High Commissioner's applause on energy optimization, productivity in Nigeria". Business Day (Nigeria).