kamfani
Carlos Luis Michel Fumero - Equipo de Aducarga.jpg
subclass oforganization, legal person Gyara
studied byeconomics, business studies, interaction science Gyara
has qualitycorporate personhood Gyara
maintained by WikiProjectWikiProject Companies Gyara

Kamfani, wannan kalma Harshen Hausa ya arota ne daga Harshen Turanci kalmar (Company). Idan akace Kamfani ana nufin guda daya kenan, Kamfanoni kuma dayawa, kamfani itace wuri ko cibiya da ayyuka ke gudana, kuma kamfani na iya zama wuri ko matattara na mutane masu aiwatar da ayyuka iri daya, ta hanyar amfani da injina ko hannu ko kuma ma batare da wani Abu ba, amma suna gabatar da tattaunawa Dan aiwatar da wani aiki ko Samar da aikin Kansa. Kamfani kan iya zama Masana'anta wato wajen da ake kera ko samar da abu. Haka zalika Kamfani kan zama wata hadaka ta mutane da suke tafiyar da wani al'amari na kasuwanci.