Kalifa Manneh (an haife shi a ranar 2 ga watan Satumba shekarata alif 1998),ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne ɗan ƙasar Gambia wanda ke taka leda a matsayin winger ga ƙungiyar Serie B ta Italiya Perugia.

Kalifa Manneh
Rayuwa
Haihuwa Serekunda (en) Fassara, 2 Satumba 1998 (25 shekaru)
ƙasa Gambiya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Carrarese Calcio (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Aikin kulob gyara sashe

Yana da shekaru 15, Manneh ya tsere daga Gambia a cikin jirgin ruwa ya sauka a Sicily a matsayin dan gudun hijira. A wannan shekarar, ya nemi Catania kuma ya shiga makarantar matasa.[1] Manneh ya fara buga wasansa na farko na gwaninta da Catania a wasan da suka tashi 0-0 a Seria C da Juve Stabia a ranar 14 ga watan Mayu 2017. [2]

A ranar 3 ga watan Janairu 2020, Carrarese ya ƙare yarjejeniyar lamuni da Catania.[3]

A ranar 15 ga watan Yuli 2021, ya sanya hannu kan kwangilar shekaru uku tare da kulob ɗin Perugia.[4] A ranar 31 ga watan Janairu 2022, an ba da Manneh aro ga kungiyar Taranto.[5]

Ayyukan kasa da kasa gyara sashe

Manneh ya fara bugawa tawagar kwallon kafa ta Gambia a wasan sada zumunci da suka doke Guinea da ci 1-0 a ranar 7 ga watan Yuni 2019.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. "La storia di Kalifa Manneh, dall'arrivo in Sicilia su un barcone alla Nazionale del Gambia" . www.lasicilia.it .
  2. "Juve Stabia vs. Catania - 14 May 2017 - Soccerway" . ca.soccerway.com
  3. "Manneh al Catania" (Press release) (in Italian). Carrarese . 3 January 2020.
  4. "Ufficiale: Kalifa Manneh" (in Italian). Perugia . 15 July 2021.
  5. "KALIFA MANNEH È UN NUOVO CALCIATORE ROSSOBLÙ" (Press release) (in Italian). Taranto . 31 January 2022. Retrieved 31 January 2022.
  6. "Kalifa Manneh ha fatto il suo debutto con la maglia del Gambia" . June 8, 2019.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe