Kader Mangane
Abdou Kader Mangane (an haife shi ranar 23 ga watan Maris ɗin shekara ta 1983) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne kuma ɗan ƙasar Senegal wanda ya taka leda a matsayin mai tsaron gida. Ya shafe yawancin aikinsa a Faransa. A matakin ƙasa da ƙasa, ya buga wa tawagar ƙasar Senegal wasanni 23 inda ya ci ƙwallo 1.
Kader Mangane | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Thiès (en) , 23 ga Maris, 1983 (41 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Faransa Senegal | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | centre-back (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 15 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 193 cm |
Aikin kulob
gyara sasheMangane ya fara aikinsa a ƙasarsa ta Senegal kafin ya koma Switzerland da Neuchâtel Xamax a cikin shekarar, 2001, inda kuma ya shafe shekaru shida. Sannan ya tafi buga wasanni biyar a Ligue 1 na Faransa, don Lens[1] a lokacin kakar shekara ta, 2007 zuwa 2008, da Rennes.[2]
A ranar 17 ga watan Yulin shekara ta, 2012, Mangane ya rattaɓa hannu kan kwangilar shekaru uku tare da kulob ɗin Al-Hilal na Saudiyya kan kuɗin da ba a bayyana ba.[3]
Ya koma ƙungiyar Sunderland ta Premier League a matsayin aro har zuwa ƙarshen kakar wasa a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta, 2013.[4]
A ranar 31 ga watan Yulin shekara ta, 2015, Mangane ya rattaɓa hannu kan Gazélec Ajaccio akan kwangilar shekara guda.[5]
Rigima
gyara sasheA ranar 21 ga watan Maris a shekara ta, 2009, yayin wasan Ligue 1 da Valenciennes ya yi wa ɗan wasan gaba Jonathan Lacourt rauni sosai a wani ƙalubale wanda ya haifar da karaya biyu na tibia da fibula. An dakatar da shi har zuwa ranar 1 ga watan Yunin shekara ta, 2009.[6]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheMangane ya sami takardar zama ɗan ƙasar Faransa a ranar 16 ga watan Mayun shekara ta, 2011.[7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.uefa.com/uefaeuropaleague/news/01c4-0e6e78b1fb28-b9093003f4b0-1000--mangane-jumps-ship-for-lens/
- ↑ https://www.uefa.com/uefaeuropaleague/news/01d0-0e6f937ded5e-b4f65389b668-1000--rennes-reach-out-for-lens-duo/
- ↑ https://www.the-afc.com/en/tournaments/clubs/afc-champions-league/935-afc-champions-league-2012/39664-Al-Hilal-signs-Abdelqader-Mangane-
- ↑ http://www.safc.com/news/team-news/2013/january/kader-signs
- ↑ https://www.lequipe.fr/Football/Actualites/Kader-mangane-au-gfc-ajaccio-off/578229
- ↑ https://www.lfp.fr/erreur404
- ↑ https://www.francefootball.fr/#!/news/2011/05/17/091550_mangane-obtient-la-nationalite-francaise.html
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Media related to Kader Mangane at Wikimedia Commons
- Kader Mangane at Soccerway
- Kader Mangane at FootballDatabase.eu