Johnson Macaba
Johnson Monteiro Pinto Macaba (an haife shi a ranar 23, ga watan Nuwambar shekara ta 1978 a Luanda), ko kuma kawai Johnson Macaba, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola. [1]
Johnson Macaba | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Luanda, 23 Nuwamba, 1978 (46 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Angola | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 186 cm |
Aikin wasan ƙwallon ƙafa
gyara sasheDan wasan ya buga wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Malatyaspor ta Turkiyya da kulob ɗin Portuguesa de Desportos da Goiás ta Brazil.
Johnson ya sanya hannu kan kwangilar shekaru uku tare da kulob ɗin Malatyaspor a lokacin rani na 2002. Ya buga wasanni bakwai a gasar, kuma an ba da rance sa ga kungiyar kwallon kafa ta Konyaspor a lokacin rani na shekarar 2003. Amma yarjejeniyar lamuni ta ci tura. Johnson ya ci gaba da zama tare da Malatyaspor, ya sake buga wasanni biyu a gasar, kafin a soke kwangilar tare a watan Mayu 2004.
Ya sanya hannu kan kwantiragin har zuwa watan Disamba 2010 tare da kulob ɗin Goiás na Brazilian Serie A a cikin watan Yuni 2006.
Ya kasance a matsayin aro zuwa ga kungiyar kwallon kafa ta Santa Cruz na Serie B a cikin watan Yulin 2007.
A farkon kakar CSL 2008, Ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Shenzhen Shangqingyin.
A cikin watan Fabrairun 2010, ya sake zuwa China kuma an ba da shi rancensa ga kungiyar kwallon kafa ta Chengdu Blades wanda CFA ta rage masa daraja daga matakin farko saboda badakalar gyara wasa.[2]
Ayyukan kasa da kasa
gyara sasheAn fi sanin Johnson a Brazil fiye da ƙasarsa ta Angola, inda jama'a suka nuna shakku game da kiran da aka yi masa na shiga gasar cin kofin Afrika na shekarar 2006.
Kididdigar kungiya ta kasa
gyara sashetawagar kasar Angola | ||
---|---|---|
Shekara | Aikace-aikace | Manufa |
2001 | 3 | 0 |
2002 | 0 | 0 |
2003 | 2 | 0 |
2004 | 0 | 0 |
2005 | 0 | 0 |
2006 | 2 | 0 |
2007 | 0 | 0 |
2008 | 0 | 0 |
2009 | 3 | 0 |
2010 | 1 | 0 |
Jimlar | 11 | 0 |
Manazarta
gyara sashe- ↑ Johnson Macaba, ex-jogador: ‘É preciso ser mais do que só atleta de futebol’ dgabc.com.br
- ↑ "成足知耻后勇不抱怨不申诉 新赛季球队招商面临 难题_国内足坛-甲A_NIKE新浪竞技风暴_新浪网" . sports.sina.com.cn . Retrieved 2017-07-18.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Johnson Macaba at National-Football-Teams.com
- Johnson Macaba at the Turkish Football Federation