John Knox shi ne mai ba da rahoto na musamman na Majalisar Ɗinkin Duniya na farko a kan ƴancin ɗan adam da al'amuran muhalli da ke aiki daga shekarar 2012 har zuwa shekarar 2018.[1] A halin yanzu Knox Farfesa ne na Dokokin Duniya a Jami'ar Wake Forest. Knox ya shahara matuƙa wajen kare haƙƙin ƴan adam tare da kula da tsaftar muhalli.[2]

John H. Knox
United Nations Special Rapporteur (en) Fassara

Rayuwa
Karatu
Makaranta Stanford Law School (en) Fassara
Sana'a
Sana'a Lauya
  • Farfesa Knox ya shahara sosai a duniya wajen aikan kare haƙƙin ƴan adam tare da yin aiyuka na musamman kamar haka[3]
  • (1994-1998) mashawarcin shari'a na Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka; lauya a cikin aikin sirri, Austin, Texas.
  • (1998-2006) Farfesa a Jami'ar Jihar Pennsylvania.
  • (2002-2005) Aiki na doka tare da ƙungiyar muhalli a Arewacin Amurka.
  • (2006-) Malami a Makarantar Shari'a ta Jami'ar Wake Forest.
  • (2008-2012) Mashawarcin shari'a ga gwamnatin Maldives.
  • (2012-2015) kwararre kan kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya a fannin muhalli.
  • (2015-) Knox ya zama mai ba da rahoto na musamman don kare haƙƙin ɗan adam da kare muhalli.

Knox ya sauke karatu tare da girmamawa daga Stanford Law School a shekarar alif 1987 ,[4] kuma ya sami BA a fannin Tattalin Arziki da Turanci daga Jami'ar Rice a 1984. [5]

A cikin shekarar 2003, ƙungiyar ƙasashen Duniya ta Amirka ta ba Knox lambar yabo ta Francis Deák, inda ta girmama shi a matsayin matashin marubuci wanda ya ba da "gudummuwa mai mahimmanci ga ƙwararrun shari'a na duniya." [6]

Manazarta

gyara sashe
  1. "John H. Knox". Archived from the original on 2019-09-11. Retrieved 2022-04-16.
  2. https://law.wfu.edu/faculty/profile/knoxjh/
  3. https://digitalcommons.law.uw.edu/wilj/vol24/iss3/6/
  4. John Knox, Former Special Rapporteur on human rights and the environment
  5. "John H. Knox". Archived from the original on 2019-09-11. Retrieved 2022-04-16.
  6. Confronting Complexity