Janio Bikel Figueiredo da Silva wanda aka fi sani da Janio Bikel, (an haife shi a ranar 28 ga watan Yunin shekarar 1995) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na Bissau-Guinean wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na kulob ɗin Seria B Vicenza, a matsayin aro daga kulob din Major League Soccer Vancouver Whitecaps FC. Ya taba buga wasa a SC Heerenveen, NEC da CSKA Sofia. Tsohon matashin ɗan wasan kasa da kasa na Portugal, yana buga wa tawagar kasar Guinea-Bissau wasa.

Janio Bikel
Rayuwa
Cikakken suna Janio Bikel Figueiredo da Silva
Haihuwa Bisau, 28 ga Yuni, 1995 (28 shekaru)
ƙasa Guinea-Bissau
Portugal
Karatu
Harsuna Portuguese language
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Portugal national under-19 football team (en) Fassara2013-201330
  N.E.C. (en) Fassara2015-
SC Heerenveen2015-201560
  Portugal national under-20 football team (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Lamban wasa 8
Nauyi 70 kg
Tsayi 173 cm

Sana'a/Aiki gyara sashe

A ranar 7 ga watan Maris din shekarar 2015, Janio Bikel ya fara wasansa na farko tare da SC Heerenveen a wasan 2014-15 Eredivisie da ADO Den Haag.[1]

A ranar 14 ga watan Yunin shekarar 2018, Janio Bikel ya sanya hannu tare da kulob din Bulgarian CSKA Sofia.[2]

Janio Bikel ya koma kungiyar Kwallon Kafa ta Major League ta Kanada Vancouver Whitecaps FC ranar 28 ga Fabrairu 2020.[3] Ya ci kwallonsa ta farko a ranar 23 ga Yuni 2021, a cikin rashin nasara da ci 2-1 a hannun LA Galaxy[4]

A ranar 21 ga Janairu 2022, Janio Bikel ya koma kulob din Vicenza na Italiya a matsayin aro.[5]

Ayyukan kasa gyara sashe

An haife shi a Guinea-Bissau kuma ya girma a Portugal, Bikel tsohon matashi ne na duniya na Portugal. Ya haɗu da tawagar kasar Guinea-Bissau a wasan sada zumunci da suka doke Equatorial Guinea da ci 3-0 a ranar 23 ga watan Maris 2022.[6]

Manazarta gyara sashe

  1. ADO Den Haag 0-1 Heerenveen". ZeroZero. 7 March 2015.
  2. Нов футболист подписа с ЦСКА" (in Bulgarian). cska.bg. 14 June 2018.
  3. Whitecaps FC acquire midfielder Janio Bikel via transfer from CSKA Sofia". Vancouver Whitecaps FC. 28 February 2020. Retrieved 28 February 2020.
  4. whitecapsfc. "GOAL: Janio Bikel nets his first of the season | Vancouver Whitecaps". whitecapsfc. Retrieved 19 July 2021.
  5. Ufficiale: Janio Bikel in biancorosso dal Vancouver Whitecaps!" (in Italian). Vicenza. 21 January 2022. Retrieved 22 January 2022.
  6. BACIRO CANDÉ APOSTA EM OITO ESTREIAS NO ONZE DOS DJURTUS CONTRA GUINÉ- EQUATORIAL". 23 March 2022.

Hanyoyin haɗi na waje gyara sashe