Jagun Jagun (Fíìmù Nàìjíŕà)
Jagun Jagun fim ne mai ban sha'awa wanda Netflix ya fitar a cikin shekara ta alif dubu biyu da Ashirin da uku 2023. Fim ne na wasan kwaikwayo, wanda Femi Adébayo da Euphoria360 Media suka shirya. Adebayo Tijani da Tope Adebayo Salami sune daraktocin wasan. Daga cikin mahalarta taron akwai Femi Adebayo, Lateef Adédiméji, Bimbo Ademoye, Faithia Balogun, Mr Macaroni, Bukunmi Oluwashina, Ibrahim Yekini da Muyiwa Ademola . Netflix ya fitar da nunin a ranar goma 10 ga watan Agusta, shekara ta alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, don kallo.[1]
Jagun Jagun | |
---|---|
Furuci | Jagun jagun |
Dan kasan | Nigeria |
Gama mulki | Femi adebayo |
Organisation | Faithia Balogun |
Mahallin tarihi
gyara sasheFim din Jagun Jagun ya samo asali ne daga labarin wani jarumi mai suna Ogundiji. Wannan jarumin yana da karfi, shahararre ne, kuma yana jawo tsoro ga garuruwan yankinsa, amma karfin wani matashi mai suna Obutija da ya zo horo domin daukar fansar mahaifinsa ya fara tsorata shi. Tunda yankin Ogundiji ya kasance ‘yan mulkin mallaka kuma ya samu nasarori da dama wajen karbe garin don ba wa shugabannin da ba su dace ba. Shigowar Abbottija da sauri ya ba shi tsoro, ya fara laluben hanyoyi daban-daban don fitar da shi daga hanya.
Mahalarta
gyara sashe- Femi Adebayo as Ogundiji
- Lateef Adémidéji as Gbotija
- Adebayo Salami (Oga Bello)
- Bukunmi Oluwashina
- Odunlade Adekola as Jigan
- Muyiwa Ademola as Oniketo
- Ibrahim Yekini Itele
- Bimbo Ademoye as Morohunmbo
- Faithia Balogun as Erinfunto
- Dayo Amusa as Ajepe
- Malam Macaroni
- Yinka Quadri
- Ibrahim Chatta
- Kunle Afod
- Yemi Elesho (Alfa Ebenezer)
- Aishah Lawal
- Dele Odule
- Ayo Ajewole (Tsohon Annabi)
- Soji Taiwo
Ci gaba
gyara sasheFim din Jagun Jagun an yi shi ne a yammacin Najeriya, kuma an kwashe sama da wata guda ana fitar da shi. Wata ‘yar fim mai suna Bukunmi Oluwashina ta bayyana cewa Femi Adebayo ya zabe ta ne a kan labarin da ya yi shekara daya da ta wuce, kafin a fara aikin fim din.
Femi Adebayo, wanda ya shirya fim din ya tabbatar da cewa aniyarsa ita ce ya sa fim din Jagun Jagun ya samu nasara fiye da wadanda ya yi a baya, har ma fiye da Sarkin barayi .
A ranar goma 10 ga watan Agusta (Agusta 10), shekarar alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, an fitar da fim ɗin Jagun Jagun akan Netflix. A cikin sa'o'i arba'in da takwas 48 da sakin ta, ta fara yaduwa a cikin Burtaniya da wasu kasashe goma sha bakwai 17. A cikin kwanaki uku da fitowar fim din, mutane miliyan biyu da dubu ɗari[2]2,100,000 ne suka kalli fim din, kuma a karshen kwanaki ashirin 20, watan Agusta, shekara ta alif dubu biyu da ashirin da uku 2023, mutane miliyan ukku da dubu ɗari bakwai 3,700,000 ne suka kalli fim din. Wannan ya sa ya zama ɗaya daga cikin manyan fina-finai goma 10 da aka fi kallo.[3]
Nassoshi
gyara sashe- ↑ https://www.pulse.ng/entertainment/movies/here-is-your-first-look-at-netflixs-jagun-jagun/2qg35f1
- ↑ Afigbo, Chinasa (2023-08-12). ""Record-breaking": Femi Adebayo's new film hits top 10 in 18 countries in 48 hrs". Legit.ng - Nigeria news. (in Turanci). Retrieved 2023-08-12.
- ↑ Netflix. "Weekly Top 10 lists of the most-watched TV and films" (in Turanci). Retrieved 2023-08-17.