Eze Igwegbe Odum (wani lokaci ana kiransa Cif Igwebe Odum) ɗan siyasar Aro ne ɗan ƙabilar Ibo da aka haifa a garin Mbaukwu na Najeriya a ƙaramar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra a yau. Igwegbe Odum, ba asalin Aro bane, amma ɗan ƙaura ne kamar yawancin mazauna Arondizuogu. Tare da ƴan uwansa, ya gudu zuwa Arondizuogu a ƙarshen ƙarni na 19. Labarin rayuwarsa ya zama batun Omenuko[1] farkon littafin tarihin Igbo wanda Pita Nwana ya rubuta. Odum ya rasu a shekara ta 1940. Ya kuma kasance suruki ga Ojiako Ezenne na Adazi. Igwegbe Odum bai taɓa komawa ƙasarsa ta Mbaukwu ba. Tare da ƴan uwansa, ya zauna a Ndi-Aniche Uno a Arondizuogu. Zuriyarsu sun haɗa da fitaccen KO Mbadiwe da ɗan uwansa Green Mbadiwe.

Igwegbe Odum
Rayuwa
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1940
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Manazarta

gyara sashe
  1. Njoku, Uzochukwu (2005). "Colonial Political Re-Engineering and the Genesis of Modern Corruption in African Public Service: The Issue of the Warrant Chiefs of South Eastern Nigeria as a Case in Point" (PDF). Catholic University of Leuven, Belgium. Archived from the original (pdf) on 2019-07-11. Retrieved 2023-04-15.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe