Ibrahim Mohammed Bukar
Ibrahim Mohammed Bukar ɗan siyasan Najeriya ne a yanzu haka mamba ne mai wakiltar mazaɓar Dikwa/Mafa/Konduga a majalisar wakilai. An haife shi a ranar 29 ga watan Janairun 1969, ya fito ne daga jihar Borno, kuma ya yi karatun digiri na farko. Ya gaji Mahmud Lawan Maina kuma an zaɓe shi a shekarar 2019 a matsayin ɗan majalisar wakilai ta ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC). An sake zaɓen shi a shekarar 2023 a karo na biyu. Daga shekarun 2011 zuwa 2014, ya zama Kwamishinan Ayyuka da Sufuri. [1] [2] [3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2025-01-06.
- ↑ "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 2025-01-06.
- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2025-01-06.