Farfesa Ibrahim Adamu Kolo (an haife shi a ranar 29 ga watan Oktoba shekara ta 1956 - ya rasu a ranar 3 watan Nuwamba shekara ta 2018) ya kasance masanin ilimin Neja. Ya rayu a karamar hukumar Mokwa ta jihar Neja .

Ibrahim Adamu Kolo
Rayuwa
Haihuwa Mokwa, 1956
Mutuwa 2018
Sana'a
Imani
Addini Musulunci

Ya halarci makarantar firamare ta UMCA da makarantar firamare ta St. Johns Anglican. Ya tafi makarantar sakandare a Kwalejin Gwamnati ta Bida kuma ya samu digiri na farko a Kwalejin Ilimi da ke Sakkwato, da Jami’ar Bayero, da Jami’ar Jos.[1]

Ya kasance malami a Kwalejin Ilimi, Jami'ar Bayero ta Kano . Ya yi aiki a matsayin Provost na Kwalejin Ilimi ta Jihar Neja, daga shekara ta 2001, zuwa shekara ta 2010.[2]

Ya yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida University, Lapai, daga shekara ta 2010, zuwa shekara ta 2015. Kwamishinan Ilimi mai zurfi Peter Sarki ya sanar da nadin Kolo a matsayin Mataimakin Shugaban Jami'ar, yana mai jaddada bukatar tsabtace jami'ar da kuma gyara lalacewar harkokin mulki. [3]

Kolo ya mutu a Minna yana da shekara 62 bayan gajeriyar rashin lafiya.[4] Janar Ibrahim Babangida ya bayyana mutuwar Kolo a matsayin "babban rashi ne ga bangaren ilimin jihar Neja da ma Najeriya baki daya".[5]

Manazarta

gyara sashe
  1. "FEDERAL UNIVERSITY OF EDUCATION, ZARIA ~ ABOUT VC". FEDERAL UNIVERSITY OF EDUCATION, ZARIA (in Turanci). Archived from the original on 26 October 2020. Retrieved 2020-10-22.
  2. Babah, Chinedu (2 March 2017). "KOLO, Prof. Ibrahim Adamu". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2020-10-22.
  3. Ibbulapai vc, "ibbulapai new vc", Daily Trust, January 2010
  4. Nmodu, Abu (5 November 2018). "Former IBB Varsity VC, Prof Kolo, Dies At 62". Leadership. Retrieved 30 July 2019.
  5. Adeyeye, Seun (5 November 2018). "IBB mourns Prof. Ibrahim Kolo". Pulse. Archived from the original on 27 June 2019. Retrieved 30 July 2019.
  • Babah, Chinedu (2 March 2017). "KOLO, Prof. Ibrahim Adamu". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 2020-10-11.