Ian Twinn
Ian David Twinn, CBE (an haife shi ranar 26 ga watan Afrilu, 1950). ɗan siyasa ne a ƙarƙashin jam'iyyar Conservative na Burtaniya.
Ian Twinn | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
21 Oktoba 2003 - 19 ga Yuli, 2004 District: London (en)
9 ga Afirilu, 1992 - 8 ga Afirilu, 1997 District: Edmonton (en) Election: 1992 United Kingdom general election (en)
11 ga Yuni, 1987 - 16 ga Maris, 1992 District: Edmonton (en) Election: 1987 United Kingdom general election (en)
9 ga Yuni, 1983 - 18 Mayu 1987 District: Edmonton (en) Election: 1983 United Kingdom general election (en) | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Cambridge (en) , 26 ga Afirilu, 1950 (74 shekaru) | ||||||||
ƙasa | Birtaniya | ||||||||
Harshen uwa | Turanci | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | University of Reading (en) | ||||||||
Harsuna | Turanci | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Wurin aiki | Strasbourg, City of Brussels (en) da Landan | ||||||||
Imani | |||||||||
Jam'iyar siyasa | Conservative Party (en) |
Farkon rayuwa da Karatu
gyara sasheAn haifeshi ranar 26 ga watan Afrilu, a shekarar 1950.
Ya yi karatu a Cambridge Grammar School for Boys (a yanzu Netherhall School), Jami'ar Wales da kuma Jami'ar Reading.
Aiki da siyasa
gyara sasheYayi aiki a matsayin lakchara.
An zabi Twinn a matsayin dan majalisa na mazabar Edmonton, ya zama dan majalisa na Conservative na farko a mukamin tun tsawon shekaru 48, kuma ya yi aiki daga 1983 har zuwa lokacin da ya rasa kujerarsa ga Andy Love na Labour a 1997.
Mataimaki
gyara sasheTwinn ya kasance mataimakin shugaban jam'iyyar Conservative daga 1986 zuwa 1988. Ya kuma zamo dan jam'iyyar Conservative na farko a Edmonton da aka sake zabar shi a karo na biyu (a cikin 1987) da kuma karo na uku (a 1992). An nada shi CBE a shekarar 2018 don hidimar siyasa da na sa kai.
A shekarar 1999, an sanya shi na biyar a cikin jerin 'yan jam'iyyar Conservative Party a London don zaɓen majalisar Turai. Jam'iyyar Conservatives ta sami kujeru hudu kawai, amma Twinn ta yi aiki a matsayin MEP na dan lokaci daga 21 ga Oktoba 2003 har zuwa zaben 2004, bayan murabus na Lord Bethell saboda rashin lafiya. Twinn ya kasance na shida a jerin 'Yan takarar jam'iyyar Conservative a zaben EU na gaba, kuma ya rasa kujerarsa yayin da 'yan Conservative suka lashe uku kacal.
Rashin nasara
gyara sasheAn jera shi a matsayi na takwas a shekarar 2009, kuma bai yi nasara a zaben shi ba.
Manazarta
gyara sasheHanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Hansard 1803–2005: contributions in Parliament by Ian Twinn
Unrecognised parameter | ||
---|---|---|
Magabata {{{before}}} |
{{{title}}} | Magaji {{{after}}} |