Hussein Ali Elshahat Ali Hassan ɗan kwallon Masar ne wanda ke buga wa ƙungiyar Al Ahly wasa a matsayin dan wasan gefe, yana iya buga wasan tsakiya na gaba.[1]

Hussein El Shahat
Rayuwa
Haihuwa Kairo, 21 ga Yuni, 1992 (32 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Egypt men's national football team (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya
Nauyi 68 kg

Aikin kulob

gyara sashe

Elshahat ya bugawa Misr Lel-Makkasa daga 2014 zuwa 2018, kafin ya koma Al Ain, inda ya lashe gasar UAE Pro League na 2017–18 kuma ya zo na biyu a gasar cin kofin duniya ta FIFA Club World Cup na 2018. Ya zura kwallo daya a wasan daf da na kusa da na karshe a wasan da suka doke Esperance Sportive de Tunis da ci 3-0.[2]A watan Janairun 2019, Elshahat ya shiga Al Ahly.[3] A ranar 4 ga Fabrairu 2021, ya ci wa Al Ahly kwallon nasara a wasan da suka doke Al-Duhail da ci 1–0 a gasar cin kofin kungiyoyin kwallon kafa ta FIFA na 2020 [4]

Ayyukan kasa da kasa

gyara sashe

An kira shi ne zuwa tawagar kasar Masar a watan Agustan 2018, domin karawa da Nijar a wasan neman tikitin shiga gasar AFCON.

Manazarta

gyara sashe