Hukumar Kula da Shara ta Jihar Ribas (RIWAMA) gwamnati ce ta Jihar Ribas dake da alhakin inganta muhalli da nufin samun ingantaccen canji mai mahimmanci a yanayin rayuwa tare da rage cututtuka ko matsalolin lafiya a jihar. Majalisar dokokin jihar Ribas ce ta kirkiro ta a shekarar 2013 kuma gwamnan jihar ya amince da shi a watan Yulin 2014. Kafin wannan, hukumar ta yi aiki a matsayin “Rivers State Environmental Sanitation Authority (RSESA)” wacce aka kafa tun a shekarar 1983 domin magance sharar kananan hukumomi da sauran batutuwa masu alaka da su.[1][2]
- ↑ Mitee, Leesi (2010). Laws of Rivers State of
Nigeria: An Encyclopaedic Guide . Worldwide
Business Resources. p. 172.
ISBN 0-9561988-1-3 . Retrieved 13 May
2015.
- ↑ Anosike, Ngozi (26 September 2012).
"RSESA Law To Be Repealed Soon…As RSHA
Gives Waste Management Bill First
Reading" . National Network. Retrieved 18
May 2015.