Harshen Dadiya
Dadiya (Dadiya, Loodiya) ɗaya ne daga cikin harsunan Savanna a arewa maso gabashin Najeriya. Ana samun su a Gombe, Adamawa da kuma jihar Taraba. Ana samun yan kabilar Dadiya ta jihar Gombe a karamar hukumar Balanga, yayin da kuma a Adamawa da Taraba ake samun bazuwar a karamar hukumar Lamurde da Karim-Lamido.
Harshen Dadiya | |
---|---|
'Yan asalin magana | 70,000 |
| |
Baƙaƙen boko | |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
dbd |
Glottolog |
dadi1249 [1] |
Ƙungiya mai suna Dadiya Community Development Association (DACODA) ce ke wakiltar al'ummar Dadiya da mazaunanta a duniya. Kungiyar dattawan Dadiya da sauran kungiyoyi masu alaka da matasa da ke taka rawa wajen ci gaban Dadiya sun hada da kungiyar ci gaban matasa ta Dadiya (DAYODA), gidauniyar ci gaban matasa ta Dadiya (DYDF) da Dadiya Success Forum.
An bayyana Sarkin/masaraucin mutanen Dadiya da 'Folo Dadiya' wanda yake zaune a hedikwatar kasar Dadiya,bambam. Mutanen Dadiya suna da zumunci da matsuguni,Suna zaune tare da sauran kabilu cikin kwanciyar hankali a Bambam da suka hada da kabilar Waja, Tula, cham da Tangale.
Mafi akasarin garuruwan Dadiya ana kiransu da sunan "Loo" wanda ke nufin ma'anar matsuguni ko gidaje. Shahararrun matsugunai a garin Dadiya sun hada da Anguwan magaji, lookwila, lookulakuli, loogolwa, looja, lofiyo, lobasi, loofa, loodib, loobware sauran kauyukan kafin bawa, dutse Dogon dutse, Mai-tunku,Bambam,Balaifi,Tunga,Delifla,Sabara,Yelwa. Nasarawa da sauransu.
Mutanen Dadiya na da bukukuwan da suke nuna al’adunsu,wasu kuma duk shekara ana yin su,wasu kuma sau dayawa kamar Yeelin, “KAL” wanda ke faruwa sau daya a shekara bakwai.
An samun mutanen Dadiya manoma ne saboda yawan gonakinsu da albarkatu, suna noman gyada, shinkafa, masara, wake da dai sauransu domin kasar tana kewaye da duwatsu da tsaunuka, mutanen Dadiya sun yi imanin cewa kasa tana da albarkar ma’adinai da yawa.
Mutanen Dadiya basu da hanyar shiga data hada kauyuka. Gwamnatin Najeriya tayi watsi da kasar Dadiya da jama’arsu domin ba su da yawa daga cikin mutanenta a gwamnatin da za su yi kamfen da kawo ci gaba a kasar ta Dadiya. Da zarar damina ta shiga, mutanen Dadiya za su rabu da sauran kasashen duniya, saboda wani babban kogi da ke gudana kusan a duk lokacin damina.
Jama'ar Dadiya a bude suke ga kowane irin cigaba mai kyau.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Harshen Dadiya". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.