Harrysong
Harrison Tare Okiri, wanda aka fi sani da Harrysong, mawaƙi ne a Najeriya, kuma marubucin waƙa kuma mai kida wanda ya zama sananne bayan waƙarsa ga Nelson Mandela da ya lashe kyautar "Mafi Girma a wata gasar waka da'a ka gudanar The Headies 2013. [1] An haifi Harrysong a Warri, Jihar Delta, Najeriya ga iyayensa yan kabilar Ijaw ne ,amma ya koma jihar Legas a 2007 bayan ya kwashee shekaru yana zaune a Port Harcourt . Kafin ya fara waka da kida, Harrysong ya kasance yana yin wasan kwaikwayo a kulob din dare har sai ya shahara,ya hadu damanyan mutane A cikin shekara ta 2014, an zabi Harrysong a cikin rukunin "Mafi kyawun masu iya waka a gasar 2014 Nigeria Entertainment Awards (A turance)bayan fitowar waƙarsa mai taswirar "Beta Pikin".[2]
- ↑ "The Headies 2013: First Photos & Full List of Winners: Olamide, Phyno, Davido, Sean Tizzle & Waje". BellaNaija. 27 December 2013. Archived from the original on 2015-09-23. Retrieved 16 October 2015.
- ↑ "2014 NEA Awards – Nominees Submission". NotJustOk. 3 April 2014. Archived from the original on 3 March 2016. Retrieved 16 October 2015.
Harrysong | |
---|---|
Yanar gizo |
www |