Hari a Pemi
A ranar 24 ga watan Disamban 2020, Boko Haram sun kai hari a Pemi, wani ƙauye wanda mafiyawan mazaunan sa Kiristoci ne a jihar Borno, arewa maso gabashin Najeriya . [1] [2] Mayakan jihadin sun iso ne a cikin manyan motoci da babura, inda suka riƙa harbin mutanen kauyen. [1] [2] Maharan sun kashe akalla mutane bakwai tare da yin garkuwa da wani limamin coci. [1] [2] Mayakan sun kona coci da asibiti da gidaje goma. [1] [2] Sun kuma wawushe kayan abinci da magunguna. [1]
Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 24 Disamba 2020 |
Adadin waɗanda suka rasu | 7 |
Perpetrator (en) | Boko Haram |