Hammed Adesope

Kwararen Dan wasan kwallon kafa ne a Najeriya

Hammed Adesope dan wasan ƙwallon ƙafa ne na Najeriya wanda ke taka leda a Buffle fc FC a Benin republic League 2020 caf champions league 2021.

Hammed Adesope
Rayuwa
Haihuwa Jahar Ibadan, 22 Oktoba 1982 (42 shekaru)
ƙasa Vietnam
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Osun United F.C. (en) Fassara2005-2007386
Kwara United F.C.2007-2009465
TDCS Dong Thap F.C. (en) Fassara2010-2013342
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya2012-201230
Kienlongbank Kien Giang F.C. (en) Fassara2013-201360
Shooting Stars SC (en) Fassara2013-2013282
Kwara United F.C.2014-2014230
Churchill Brothers S.C. (en) Fassara2014-201470
Al-Orouba SC (en) Fassara2015-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga baya

Rayuwar mutum

gyara sashe

Mahaifiyar Hammed ta bada gagarumar gudun mawa a rayuwarsa a matsayin dan wasan ƙwallon ƙafa kuma ita ce ta ƙarfafa shi ya zama ɗan ƙwallon ƙafa. Burinsa ne ya zama ɗaya daga cikin 'yan wasan da suka yi nasara a duniya.

Aikin kulob

gyara sashe

Hammed ya fara sana'an kwalaon kafa a shekara ta 2000 tare da Nijeriya kulob, Balogun Owoseni FC. A cikin shekara ta 2002, ya koma Ila-Orangun FC wanda ya yi wasa anan har zuwa shekara ta 2005. Daga nan ya koma kulob din National League na Najeriya , Prime FC inda ya yi wasa har zuwa 2007. Daga nan ya koma kulob din Premier League na Najeriya , Kwara United FC a 2007 inda ya yi wasa har zuwa shekara ta 2009.

Ya fara ficewa daga Najeriya a shekarar 2009 zuwa Vietnam, inda ya sanya hannu kan kwantiragi na dogon lokaci tare da TDCS Đồng Tháp FC Ya fara buga wasansa na V.League 1 a ranar 22 ga watan Janairun shekara ta 2011 a wasan da suka tashi 0-0 da Navibank Sài Gòn FC kuma ya zira kwallon sa ta farko a ranar 10 ga watan Afrilu shekara ta 2011 a wasan da suka tashi 2-2 da Khatoco Khánh Hòa FC Ya zura kwallaye 2 a wasanni 24 da ya buga a 2011 V-League.

Ya fara fitowa na farko na 2012 V-League a ranar 29 ga Afrilu 2012 a nasarar 4-1 akan Vissai Ninh Bình FC Ya buga wasanni 10 a 2012 V-League.

Manazarta

gyara sashe