Dr. Hadiza Nuhu (OON) Babbar Malama ce a sashen Pharmacognosy da harhaɗa magunguna a Jami'ar ABU Zaria . Ta sha samun lambobin yabo bisa ga aikin ta na samar da magunguna. [1]

Hadiza Nuhu
Rayuwa
Haihuwa jihar Kano, 1965 (58/59 shekaru)
Sana'a

Nuhu shahararriyar farfesa ce wanda ta lashe lambar yabo a Furofesa kuma sananniya a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya.

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

Haifaffiyar jihar kano 23 ga watan agusta 1965. Ta yi karatun digirin-digirgir a fannin Pharmacognosy daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya da kuma takardar shedar karatun ƙere ƙere a Kwalejin Newcastle da ke Burtaniya. [2]

Maganin HERB 25

gyara sashe

A shekara ta 2009, Dakta Hadiza ta samar da maganin Herb 25, maganin yaƙi da zazzaɓin cizon sauro wanda ta bayyana a matsayin, ingantaccen shiri ne na hada-hadar ganyayyaki da aka yi amfani da su a Najeriya bisa al'ada don magance zazzaɓin cizon sauro. [3]

Herb 25 amintacce ne na maganin zazzabin cizon sauro don magance malaria mai juriya ta Chloroquine. Maganin yana da lambar amincewa ta NAFDAC. An rarraba shi cikin buhunan shayi, mai sauƙin amfani a ruwan zafi. Wannan zai zama karo na farko da wata Jami'a a Najeriya za ta yi nasarar samar da irin wannan magani. [4] [5]

Manazarta

gyara sashe