Gonzalo Gerardo Higuaín
Gonzalo Gerardo Higuaín (An haifeshi ranar 10 ga watan Disamba, 1987). Ya kasance tsohon dan wasan gaban ƙasar Ajantina ne ana masa lakani da suna Elpipita ko kuma Pipa. Higuain yana daya daga cikin jerin yan gaba na tsakiya da suka fi kowa a lokacin sa. Dan wasan ya kasance masanin raga wanda idonsa idon raga sannan ya mori kirar jiki ga karfi kuma ga karfin buga kwallo.
Gonzalo Gerardo Higuaín | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Gonzalo Gerardo Higuaín | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Brest, 10 Disamba 1987 (36 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Argentina Faransa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifi | Jorge Higuaín | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ahali | Federico Higuaín (mul) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Yaren Sifen | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 89 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 184 cm |
Yaci kofinan turai har guda shida inda daga cikin kofinan akwai wadanda yaci a gasar Laliga da kuma gasar Serie A.
Higuain ya fara rayuwar kwallon shi a wata kungiya ta kasar Ajantina wato kungiyar kwallon kafa ta River Plate kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid a watan Junairu shekarar alif 2007. Lokutan da yayi a kasar ta Sifaniya, yaci gasar Laliga har sau ukku tare da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid inda ya zama daya daga cikin manyan yan gaba na duniya ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Napoli ta kasar Italiya akan jumillar kudi £40 miliyan a shekarar alif 2013 inda yaci gasar Coppa Italiya a shekarar dan wasan ta farko. A shekarar alif 2015 zuwa shekara ta alif 2016, dan wasan ya samu nasarar jefa kwallaye 36 a shekarar kuma har ya lashe gasar Copacannoniere inda suka zura kwallaye iri daya a gasar.
Kungiyar dake rike da kambu na lashe gasar wato kungiyar kwallon kafa ta Juventus, sun kulla yarjejeniya da dan wasan akan jumillar kudi £90 miliyan a shekarar alif 2016 inda cinikin ya zama babban cinikin da babu kamar sa kuma babu dan wasa mai tsadar Higuain din a duk gasar gaba daya. Komawarshi Sabuwar kungiyar shi ta Juventus ya lashe gasar har sau biyu. Kuma ya wakilci kungiyar tashi a wasan karshe da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid sannan yaje zaman aro a wasu kungiyoyin, irin su ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea da kuma kungiyar kwallon kafa ta Ac Milan. Dan wasan ya samu nasarar lashe Kofin zakarun nahiyar Turai. Daga baya kuma dan wasan ya koma ƙungiyar dake yankin Latin wato kungiyar kwallon kafa ta Inter Miami a shekarar alif 2020 kafin ya ajiye kwallo a shekarar alif 2022.
A fannin kasa kuma, Higuain ya fara wakiltar kasar tashi a shekarar alif 2009[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Acta del Partido celebrado el 01 de junio de 2013, en Madrid" [Minutes of the Match held on 1 June 2013, in Madrid] (in Spanish). Royal Spanish Football Federation. Archived from the original on 3 September 2019. Retrieved 18 June 2019.