Goje
Goje (Sunan wani abin kida na Hausawa ) yana daya daga cikin sunaye iri-iri na goge iri daya ko masu zare kala daya a Afirka ta Yamma, wadanda yaruka irin Yarbawa suke yin kida dashi “ kidan Sakara ” da kuma wasu a yammacin Afirka wadanda ke zaune a Sahel.Fatar maciji ko kadangaru ko kuma wata fatar dabbar daban ake amfani da su wajen hada goge. Ana wasa da goje da zaren baka.
Goje | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | bowed string instrument (en) |
An fi amfani da goje don inganta waka, kuma yawanci ana yin goge ne a matsayin kayan kida, ko da yake kuma tana tayi fice a cikin yaruka da sauran kayan zaren na Afirka ta Yamma, da kade-kade, ciki har da Shekere, gangunan kwarya, gangunan magana.
Ana daurawa kayan kidan wasu abubuwan al’adu daban-daban na yankin Sahel kafin zuwan Musulunci, don mallakar aljanu, kamar al’adun Bori da Hauka na Maguzawan Hausawa, Zarma, Borori, da Songhay. Wadandan kayan kidan ana daraja su sosai kuma ana amfani da su suna da alaka da duniyar ruhu, ko kuma a matsayin mai daukar muryoyin da ke nufin ko daga duniyar ruhu.
Sunaye daban-daban da ake kiran goje da su, da yarukan Afirka sun haɗa da goge ko goje ( Hausa, Zarma ), gonjey ( Dagomba, Gurunsi ), gonje, ( Mamprusi, Dagomba ), njarka ( Songhay ), n'ko ( Bambara, Mandinka da sauran su Mande. harsuna ), riti ( Fula, Serer ), da nyanyeru ko nyanyero.
A cikin Hausawa, akwai wani abin kida karami mai suna kukkuma, wanda amfaninsa yana da alaka da wasu ayyuka na wasa, amma ana wasa dashi kamar goje mai dan girma da daraja.
Manazarta
gyara sashe- Liner notes by Steve Jay in "Ghana: Ancient Ceremonies: Dance Music & Songs," Nonesuch Explorer Series, 1979, re-released, 2002. catalog number or ASIN: B00006C75Y