Gogo Chu Nzeribe
Gogo Chu Nzeribe ɗan ƙungiyar ƙwadagon Najeriya ne kuma jagoran ƙungiyar gurguzu ta ƙasar a lokacin yunƙurin neman ƴancin kai a shekarun 1950.[1] Ya kasance babban sakataren ƙungiyar ƴan kasuwa ta Najeriya, wanda a lokacin shugaban ƙasa Michael Imoudu ya jagoranta. Sojojin da ke biyayya ga ɓangaren tarayya sun kashe Nzeribe a cikin shekarar 1967 a lokacin rikicin shekarun 1960. Kafin rasuwarsa, gwamnatin Yakubu Gowon ta kama shi tare da tsare shi a Barrack Dodan.
Gogo Chu Nzeribe | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 1967 |
Karatu | |
Makaranta | King's College, Lagos |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da trade unionist (en) |
Yana da ɗiya mace tare da marubuciyar Najeriya, Flora Nwapa. [2]
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Nzeribe a cikin iyali mai wadata kuma ya halarci Kwalejin King dake Legas. Ya koma ƙungiyar ƙwadago ne sakamakon sha’awar da yake da ita a gwagwarmayar neman ƴancin kai a Najeriya. Ya fara shirya gangamin ɗalibai da ma'aikata domin nuna adawa da mulkin mallaka.[3]
Manazarta
gyara sashe- ↑ American Assembly. United States and Africa, American Assembly, Ayer Publishing, 1970. p 91. 08033994793.ABA
- ↑ Chikwenye Okonjo Ogunyemi. African Wo/Man Palava: The Nigerian Novel by Women, University of Chicago Press, 1996. p 134. 08033994793.ABA
- ↑ Steven L. Jacobs, Samuel Totten. Pioneers of Genocide Studies (Clt), Transaction Publishers, 2002. p 142. 08033994793.ABA