Gidauniyar Rochas

Kungiyar tallafi a Najeriya

Gidauniyar Rochas ta kasance hukuma ce ta tallafi wacce bata gwamnati bace kuma bata neman riba ba. An kirkire ta a shekarar 1998[1] tare da babbar hedikwatar ta a Abuja, Najeriya. Rochas Okorocha ne ya kafa kungiyar, ya kasance dan' kasuwa a Najeriya, mai taimako kuma dan'siyasa.[2][3][4] Gidauniyar Rochas nada gidauniyoyi da dama dake karkashin ta, wadanda suka hada da Kwalejin Gidauniyar Rochas ta Afirka (Rochas Foundation College of Africa). Gidauniyar Rochas tafi mayar da hankali ne a tallafawa, karfafawa da taimakon yara marasa karfi dake yawo akan titunan Afirka dan basu damar samun ilimi mai inganci ta hanyar taimakon ilimi na scholarship a kyauta.[5][6] Kungiyar na da makarantu 21 wadanda ba'a biyan kudi guda 12 acikin jihohin Najeriya. A watan Oktobar shekarar 2019, Gidauniyar Rochas ta fitar da kudi kimanin Naira biliyan daya (kusan Dalar amurka miliyan 360) dan taimakon yara da basu zuwa makaranta a Najeriya.[7] A shekarar 2018, ta bayar da tallafin karatu (scholarships) ga yara dubu daya dake a wuraren da aka kebe yan'gudun hijira (Internally Displaced Persons IDP) dake a Jihar Benue.[8][9]

Gidauniyar Rochas
Bayanai
Iri foundation (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
Mulki
Tsari a hukumance foundation (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 1998
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.


Manazarta

gyara sashe
  1. Nasir, Jamilah (16 February 2018). "Flavour to perform as Rochas Foundation marks 20th anniversary". The Cable. Missing or empty |url= (help)
  2. IV, Editorial (2019-09-27). "Rochas College celebrates founder's 57th birthday in Kano". Blueprint.
  3. Published. "Okorocha floats READ". Punch Newspapers.
  4. Chukwu, Ebere (2017-11-08). "Rochas Okorocha Foundation hosts Liberia's Ellen Johnson Sirleaf Thursday". TODAY.
  5. "Rochas Foundation gives scholarships to 899 students in plateau". Daily Nigerian. 2019-09-27. Archived from the original on 2020-11-30. Retrieved 2020-08-18.
  6. "I've Never Experienced Anything Like Rochas Foundation – Ellen Johnson-Sirleaf". Channels Television.
  7. "Rochas Foundation earmarks N1bn to tackle out of school children challenge". Pulse Nigeria. 2019-10-23.
  8. says, Ezekiel Okeke (2018-02-26). "Killings: Rochas Foundation offers scholarship to 1,000 Benue children". The Sun Nigeria.
  9. admin (2018-02-26). "Reprieve for Benue IDPs as Rochas Foundation Offers 1,000 Scholarships to Displaced Children". THISDAYLIVE.