Gidajen Gwarimpa Estate
Gwarimpa Estate yankin gidaje ne na zamani da ke a a yankin Phase 3, a babban birnin Najeriya, Abuja.[1][2] Ita ce mafi girman gidajen haya a Najeriya da yammacin Afirka. Manyan gidajen sun ƙunshi wasu kyawawan ƙirar gine-gine tare da hanyoyin sadarwa masu kyau da gidaje masu tsada. [3]
Gidajen Gwarimpa Estate | |
---|---|
Wuri | |
Coordinates | 9°06′43″N 7°23′53″E / 9.11194108°N 7.39808769°E |
|
Tarihi
gyara sasheTarihin gidan ya samo asali ne tun lokacin gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha, lokacin da aka gina shi. Gidan tun daga lokacin ya kasance yana bunƙasa tare da haɓaka a yawan jama'a.[1][3]
Labarin kasa
gyara sasheGidajen Gwarimpa na nan akan wani fili mai faɗin hekta 1090 tare da wuraren zama guda 7,[4] waɗanda manyan hanyoyi suka keɓe. Rukunin gidaje na Gwarimpa yana makwabtaka da Katampe da Jahi a arewa maso gabas, Kado a gabas, Jabi a kudu maso gabas da Life Camp a kudu. Yayin da a yamma da arewa maso yamma akwai Karsana da Dawaki & Kubwa.
Manyan titunan yankin sun hada da titin Murtala Mohammed daga gefen arewacin gundumar da kuma titin Ahmadu Bello zuwa kudu. Akwai wata hanyar Ring 2 wacce ta hada Gwarimpa zuwa bayan birnin Abuja kamar Galadimawa.[1]
Manyan otal-otal a cikin rukunin gidaje sun haɗa da irinsu; Benysta Hotel Grarimpa, House 12 Studios da Suites, Blue Palazzo Hotel, Cuzzi, Sefcon Suites da Apartments, Starview Palace Hotel, Trafford Hotel, Purple Tulip Hotel, Frankeys Haven Suite da Sumed Suite Annex.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 "Gwarinpa Abuja | Area Guide". Villa Afrika Realty. Retrieved 2022-04-12.
- ↑ "List of Property in Gwarinpa, Abuja (764 available)". nigeriapropertycentre.com. Retrieved 2022-04-12.
- ↑ 3.0 3.1 "Gwarimpa: Nigeria's largest housing estate battles distortions". Daily Trust. 2018-10-22. Retrieved 2022-04-12.
- ↑ "Gwarinpa: ugly face of Abuja's largest estate". The Nation Newspaper. 2013-11-25. Retrieved 2022-04-12.
- ↑ "Agoda.com: Smarter Hotel Booking". www.agoda.com. Retrieved 2022-04-12.