Gabriel Magalhães
Gabriel dos Santos Magalhães An haifeshi a ranar 19 ga watan Disamba 1997 wanda aka fi kiranshi da suna Gabriel. Kwararren dan wasan kasar Brazil ne wanda yake taka leda a matsayin dan baya. Dan wasan ya kasance yana buga gasar premier league ta ingila, inda yake taka leda a kungiyar Arsenal. Sannan kuma babban dan wasa ne da yake wakiltar kasar brazil.[1]
Gabriel Magalhães | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Gabriel dos Santos Magalhães | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | São Paulo, 19 Disamba 1997 (27 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Brazil | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 6 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 78 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 190 cm |
Rayuwar kwallo
gyara sasheAvai
gyara sasheAn haifi dan wasan ne a Prituba District na Sao paulo. Tun yana da shekaru goma sha ukku 13, ya fara doka ma kungiyar ta avai wasa. Saidai kuma ya dawo Saulo saboda yawan jinya ta gida. Sai dai ya kuma sake dawowa Avai din bayan wasu yan satuttuka. Ya fara rattaba hannu a matsayin kwararren dan wasa a shekaru 16. Yajevwata kungiya ne wadda ta samu damar tsallakewa zuwa babbar gasa ta Brazil a shekarar alif dubu biyu da goma sha bakwai 2017.[2]
Lille
gyara sasheA ranar 31 ga watan Junairu 2017 dan wasan ya koma taka leda a Gasar League 1 inda yake taka leda a kungiyar lille inda ya rattaba hannu da kwantiragin shekaru hudu da rabi. Lokacin da ya isa a garin, ya koya ma kansa yaren faransaci saboda mafi yawancin tattaunawa da ake dashi da faransaci akeyi. Bayan ya buga wasanni da yawa a kungiyar ta lille, ya ya tafi zaman aro a kungiyar troyes. Kafin ya koma kungiyar dake kasar Croatia wato dynamo zegreb inda ya buga wasa daya kacal a kowace kungiyar.[3]
Dan wasan ya dawo lille 2018 inda ya fara wasanshi na farko a ranar 10 ga watan Fabrairu 2019 a wasan da ya buga da kungiyar hamayya Guingamp wadda tayi rashin nasarar ketarawa gasa ta kasanta inda suka samu nasarar lashe wasan daci 2-0. Dan wasan yaci kwallonsa ta farko ne inda suka fafata da kungiyar P. S. G, inda suka zazzaga ma P. S. G din kwalaye har 5-1 wanda aka buga a 14 April 2019.
Shekara ta gaba, ya zama mai doka wasanni a koda yaushe kuma ko wane wasa za a buga dole sai ansashi matukar anaso a samu nasara a wasan.[4]
Arsenal
gyara sasheA ranar 1 ga watan September 2020 Arsenal suka wallafa a shafinsu na daukar dan wasan da yarjejeniyar kwantiragi mai tsawo da akayi da dan wasan da kuma kungiyar. An sayi dan wasan da jumillar kudi kimanin £27m.[5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Mewis, Mark WhiteContributions from Joe; updated, Steven Chicken last (15 September 2023). "Ranked! The 10 best centre-backs in the world". fourfourtwo.com. Retrieved 27 October 2024
- ↑ Avaí Futebol Clube " Gabriel" (in Portuguese). 25 April 2017. Archived from the original on 25 April 2017. Retrieved 28 August 2020
- ↑ "Gabriel dos Santos Magalhães" (in French). Lille OSC. Archived from the original on 31 March 2020. Retrieved 3 February 2020
- ↑ "Gabriel: 5 things on Lille's up-and-coming Brazilian defende". Ligue 1. Retrieved 28 August 2020.
- ↑ Gabriel Magalhaes: Arsenal sign Brazilian defender from Lille". BBC Sport. 1 September 2020. Retrieved 12 September 2020