Francisca Ikhiede
Francisca Ikhiede (An Haife ta a ranar 17 ga watan Janairu 1996) 'yar wasan volleyball ce ta Najeriya wacce ke taka leda a kungiyar Customs ta Najeriya da kuma kungiyar kwallon raga ta mata ta Najeriya.
Francisca Ikhiede | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Kaduna, 17 ga Janairu, 1996 (28 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | volleyball player (en) |
Rayuwa
gyara sasheAn haifi Ikhiede a Kaduna a shekarar 1996.[1] Ta taba bugawa kungiyar kwallon ragar hukumar kwastam ta Najeriya wasa.[2]
Ikhiede tana taka leda a kungiyar kwallon volleyball "b" ta bakin teku (Beach volleyball) ga kungiyar kwallon ragar mata ta Najeriya.[3] A farkon shekarar 2019 ta kasance a Yaoundé a Kamaru inda ita da Tochukwu Nnourge suka lashe lambar zinare a gasar kwallon ragar beach ta Camtel International. Sun samu nasara a wasan karshe duk da murnan da jama'a suka yi domin adawarsu ita ce ta Kamaru. [4]
Tawagar Najeriya ta zo ta biyu a lokacin da Kenya ta samu gurbin shiga gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2020 da aka dage. Kasashen Afirka hudu ne kawai suka tura tawaga zuwa gasar Olympics. [5] Tawagar Kenya ta kasance Yvonne Wavinya, Brackcides Agala, Phosca Kasisi da Gaudencia Makokha. Tawagar Najeriya ta sha kashi a gasar cin kofin nahiyar Afrika da aka yi a Morocco a 2021. [5] Tawagar Kenya ta Wavinga da Kasisi ta doke Tochukwu Nnoruga da Albertina Francis da ci 2-0 yayin da Agala da Makokha suka doke sauran 'yan Najeriya biyu na Ikhiede da Amara Uchechukwu da ci 2-1. [5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ www.bvbinfo.com http://www.bvbinfo.com/ player.asp?ID=19378 . Retrieved 2021-07-20.
- ↑ "Francisca Ikhiede » clubs" . Women Volleybox . Retrieved 2021-07-20.
- ↑ "Beach V/ball: Nigeria women team to miss Tokyo Olympics" . ACLSports . 2021-06-27. Retrieved 2021-07-20.
- ↑ "Team Nigeria women's team wins beach volleyball championship in Cameroon" . The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News . 2019-01-01. Retrieved 2021-07-22.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 volleyballworld.com. "Argentina, China, Cuba and Kenya take Olympic berths" . volleyballworld.com . Retrieved 2021-07-20.Empty citation (help)