Figueres
Figueres (Da harshen Katalanci 'bishiyar', Furuci a yaren Katalanci: [fiˈɡeɾəs], [fiˈɡeɾes]; Spanish: Figueras, [fiˈɣeɾas]) itace babbar birnin comarca na Alt Empordà, ia gundumar Girona, Catalonia, Hispaniya.
Figueres | |||||
---|---|---|---|---|---|
|
|||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ispaniya | ||||
Autonomous community of Spain (en) | Katalunya | ||||
Functional territorial area (en) | Comarques Gironines (en) | ||||
Comarca of Catalonia (en) | Alt Empordà (en) | ||||
Babban birnin |
Alt Empordà (en)
| ||||
Babban birni | Figueres (en) | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 47,879 (2023) | ||||
• Yawan mutane | 2,480.78 mazaunan/km² | ||||
Home (en) | 218 (1553) | ||||
Harshen gwamnati | Catalan (en) | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Mancomunitat de Municipis Comunitat Turística de la Costa Brava (en) da Q107554324 | ||||
Yawan fili | 19.3 km² | ||||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Manol river (en) | ||||
Altitude (en) | 39 m | ||||
Sun raba iyaka da |
Cabanes (en) El Far d'Empordà (en) Llers (en) Peralada (en) Vila-sacra (en) Vilabertran (en) Vilafant (en) | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Muhimman sha'ani |
Siege of Figueras (en)
| ||||
Tsarin Siyasa | |||||
• Mayor of Figueres (en) | Jordi Masquef (en) (17 ga Yuni, 2023) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Lambar aika saƙo | 17600 | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Tsarin lamba ta kiran tarho | 972 | ||||
INE municipality code (en) | 17066 | ||||
IDESCAT territorial code in Catalonia (en) | 170669 | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | ca.figueres.cat |
A garin aka haifi mai zane Salvador Dalí, kuma akwai gidan tarihi mai suna Teatre-Museu Gala Salvador Dalí, babban gidan kayan gargajiya wanda Dalí da kansa ya tsara wanda ke jan hankalin baƙi da yawa. Har ila yau, a nan aka haifi Narcís Monturiol, wanda ya fara yin nasarar ƙirƙira jirgin ruwa mai ƙarfi na farko a duniya. Har ila yau, a nan ne aka haifi Mónica Naranjo, ɗaya daga cikin mawaƙan Hispaniya da tafi kowa shahara acikin Mutanen Espanya a tsakanin 1990s da 2000s.
Tarihi
gyara sasheSunan garin ya samo asali ne daga Ficaris, na asalin Visigoth. A shekarar 1267, Sarki James na na Aragon ya amince da haƙƙin fuero, amma bayan shekaru huɗu Count Ponç IV na Empúries ya cinnawa garin wuta.
A cikin 1794 Figueras ta mika wuya ga Faransa, amma an sake dawo da ita a cikin shekarar 1795. A lokacin Yaƙin Peninsular Turawan Faransa ne suka kwace yankin a 1808, Mutanen Sipaniya suka sake kwato shi a 1811, Faransawa suka sake karbe shi a cikin wannan shekarar. [1]
A lokacin yakin basasa na Sipaniya, garin ya zamo amintacce ga gwamnatin Republican, kuma jiragen saman Italiya na Nazi da na Fascist sun ta jefa bama-bamai akai-akai.[2]
Yana daya daga cikin garuruwan Kataloniya da aka fi yi masu ruwan bama-bamai a lokacin yakin basasa, a shekarar 1938, kuma, musamman, a farkon shekarar 1939, lokacin da dubban mutane suka ratsa cikin garin kan hanyarsu ta gudun hijira. Tabbas ba za a iya sanin adadin wadanda harin bam ya rutsa da su ba, amma zai kai kusan 400.[3]
Gwamnatin Republican ta Hispaniya ta gudanar da taronta na ƙarshe na yakin basasa (ranar 1 ga Fabrairu 1939) a gidan kurkukun Sant Ferran Castel .
Garin Figueres ta farfado tun daga 1950s, tana ƙarfafa tattalin arzikinta da masana'antun yawon shakatawa.[4]
Muhimman wurare
gyara sashe- Sant Ferran Castle, wanda aka gina a cikin 1753 a lokacin mulkin Ferdinand VI na Spain, a wurin wani gidan zuhudu na Capuchin. Yana da shimfidar pentagonal, tare da jimlar kewayen 5.6 kilometres (3.5 mi) .
- Ikilisiyar Parish na St. Peter, a cikin Gothic . Yana da nave guda ɗaya tare da ɗakin karatu na gefe.
- Teatre-Museu Gala Salvador Dalí (ƙarni na 19, an sabunta shi a cikin 1960s). Ya haɗa da hasumiya daga tsohuwar ganuwar.
- Gidan kayan tarihi na fasaha na Empordà, gidan kayan gargajiyar fasaha tare da ɗaruruwan na'urorin buga rubutu na tsoho
- Museu de l'Emportda
Sanannun mutane
gyara sashe- Narcís Monturiol (1819-1885), injiniyan jirgin ruwa na farko kuma mai ƙirƙira.
- Salvador Dalí (1904-1989), mashahurin mai fasaha a duniya
- Montserrat Minobis da Puntonet (1942 – 2019), yar jarida ta mata
- Montserrat Vilà (an haife shi a shekara ta 1964), masanin ilimin halitta
- Mónica Naranjo (an haife shi a shekara ta 1974), mawaƙa kuma mai watsa shirye-shiryen talabijin
- Dídac Lee (an haife shi a shekara ta 1974), ɗan kasuwa, tsohon memba na hukumar FC Barcelona
- Maverick Viñales (an haife shi a shekara ta 1995), ɗan tseren MotoGP
- Sílvia Soler (an haifi 1961), marubuci kuma ɗan jarida
Garuruwan Twin - garuruwan 'yan'uwa
gyara sasheAn haɗa Figueres tare da:
- Alcalá la Real, Spain (1989)
- Marignane, France (1968)
- Kalisz, Poland (1986)
- St. Petersburg, United States (2011)
Nassoshi
gyara sashe- Nassoshi
- ↑ One or more of the preceding sentences incorporates text from a publication now in the public domain: Chisholm, Hugh, ed. (1911). "Figueras". Encyclopædia Britannica (11th ed.). Cambridge University Press.
- ↑ "Figueres, la Gernika de Catalunya". Publico (in Spanish). 2013-04-03. Retrieved 2020-01-03.
- ↑ "ICIP participates in the historical memory project "(silences) Figueres under the bombs". International Catalan Institute for Peace. Generalitat de Catalunya". International Catalan Institute for Peace. Retrieved 2020-01-03.
- ↑ "Castell de Sant Ferran | Figueres, Spain Attractions". Lonely Planet. Retrieved 2020-01-03.
- Adabi
- Panareda Clopés, Josep Maria; Rios Calvet, Jaume; Rabella Vives, Josep Maria (1989). Guia de Catalunya, Barcelona: Caixa de Catalunya. ISBN 84-87135-01-3 (Spanish). ISBN 84-87135-02-1 (Catalan).
- Majalisar Figueres : Majalisar Figueres (Catalan)
- Shafukan bayanan gwamnati (in Catalan)
Samfuri:Geographic locationSamfuri:Alt EmpordaSamfuri:Municipalities in Girona