Federal College of Education (Technical), Umunze

Federal College of Education (Technical), Umunze kwalejin ilimi ce a Nijeriya da aka gina a garin Umunze, Orumba ta Kudu karamar Jihar Anambra, Nigeria . Tana da alakar hadin gwiwa da Jami'ar Nnamdi Azikiwe inda ta aro kuma take gabatar da darussan karatun digiri na farko a cikinta.

Federal College of Education (Technical), Umunze
Bayanai
Iri higher education institution (en) Fassara
Ƙasa Najeriya
fcetumunze.edu.ng

Dalibai gyara sashe

A 'yan kwanakin bayan nan, kwalejin tana da yawan mutane kusan 6,000 a cikin tsarin karatunta na NCE, 1,200 a Degree da kuma ɗalibai 455 a babbar dufulomar Ilimi.

Darussa gyara sashe

Kwalejin na ba da kwasa-kwasai da yawa ƙarƙashin tsangayoyin ta masu zuwa kamar haka:

1. Tsangayar Ilimin Kasuwanci

2. Tsangayar Ilimi da Fasaha

3. Tsangayar Noma da Ilimin Girki da Tattalin Gida

4. Tsangayar Ilimin Masana'antu

5. Tsangayar Koyon Ilimin Kwamfuta da Ilimin Kimiyya

6. Tsangayar Kwarewar Fasahar Zane-zane

7. Makarantar karatun bai ɗaya da Pre-NCE

Manazarta gyara sashe