Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina
Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Katsina cibiyar ilimi ce ta gwamnatin tarayya da ke Katsina, Jihar Katsina, Najeriya.
Kwalejin Ilimi ta Tarayya, Katsina | |
---|---|
| |
Excellent in Education | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
Federal College of Education, Katsina |
Iri | school of education (en) da jami'a |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1976 |
fcekatsina.edu.ng |
Tana da alaƙa da Jami'ar Bayero Kano don karatun digiri. Shugaban makarantar na yanzu shine Aliyu Idris Funtua.[1]
Tarihi
gyara sasheAn kafa Kwalejin Ilimi ta Tarayya (Technical) Katsina a shekara ta 1976.[2]
Laburare
gyara sasheLaburaren Kwaleji, ɗakin karatu ne wanda aka kafa a shekara ta 1975 a matsayin babban ɗakin karatu na kwalejin. Laburare na da litattafai sama da dubu 50,000, gami da wurin zama da zai iya ɗaukar mutane 500 alokaci guda, tare da kayan lantarki - ɗakin karatun na da kwamfutoci sama da 100 gami da sabis na shiga yanar gizo ko intanet.[3] Akwai isassun kayan aiki a dakin karatun don samun sauƙin bayanai game da dalibai, kuma suka dace da darussan da ake koyawa a kwalejin. Babban ɗakin karatu ne ke kula da sauran ɗakunan karatu na sashe a cikin makarantar.[3]
Darussa
gyara sasheCibiyar tana ba da darussa kamar haka;[4]
- Ilimin Kimiyyar Noma
- Ilimi da Lissafi
- Fine And Applied Arts
- Ilimin Kimiyya
- Ilimin Gina Fasaha
- Ilimi da Ingilishi
- Ilimin Kwamfuta
- Ilimi da Hausa
- Ilimi da Larabci
- Ilimin Fasaha
- Ilimin Halitta
- Ilimi da Ilimin zamantakewa
- Tattalin Arzikin Gida da Ilimi
- Hadaddiyar Kimiyya
- Ilimin Kasuwanci
- Karatun Ilimin Firamare
Alaƙa da Tsari
gyara sasheCibiyar tana da alaƙa da Jami'ar Bayero Kano don bayar da shirye-shiryen da za su kai ga samun digiri na farko (B.Ed.) a;
- Ilimi da Physics
- Ilimi da Chemistry
- Ilimi da Ingilishi
- Ilimin Jiki da Lafiya
- Ilimi da Ilimin Addinin Musulunci
- Ilimi da Larabci
- Ilimi da Biology
- Ilimi da Lissafi
- Ilimi da Hausa
Makarantar baya ga shaidar kwalin NCE da take badawa kuma ana degree (undergraduted) a makarantar. Kuma cibiyar tana dora ɗalibai zuwa wuraren aiki don samun ƙwarewar aiki ta hanyar shirin SIWES.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Just In: President Buhari reappoints Dr. Aliyu Idris Funtua as Provost FCE Katsina". Katsina Post (in Turanci). 2020-07-10. Archived from the original on 2021-08-13. Retrieved 2021-08-13.
- ↑ "HISTORY – FEDERAL COLLEGE OF EDUCATION KATSINA" (in Turanci). Retrieved 2021-08-13.
- ↑ 3.0 3.1 "Federal College of Education, Katsina". fcekatsina.edu.ng. Retrieved 2022-12-05.
- ↑ "List of Courses Offered at Federal College Of Education Katsina (FCEKATSINA)". Nigerian Scholars (in Turanci). 2018-03-06. Retrieved 2021-08-13.