Fatin Youssef Bundagji

Yar kasuwar ƙasar Saudiyya

Fatin Bundagji (an haife ta a shekara ta 1958) yar kasuwa ce kuma memba ce a kwamitin gudanarwa na Rukunin Cibiyar Kasuwanci da Masana'antu na Jeddah.[1]

Fatin Youssef Bundagji
Rayuwa
Haihuwa 1958 (65/66 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Harshen uwa Larabci
Karatu
Makaranta Jami'ar Sarki Abdulaziz
Harsuna Larabci
Sana'a
Sana'a ɗan kasuwa

Karatu da Aiki gyara sashe

Ita abokiyar aikin ƙungiyar Eisenhower fellow ce. Ta yi digiri na biyu a fannin adabin turanci a Jami'ar King Abdul Aziz.

Ayyuka gyara sashe

A shekara ta 1998 aka naɗa ta don kafa rukunin mata na farko a cibiyar kasuwanci da[2] masana'antu ta Jeddah matsayin da ya kasance irinsa na farko ga matan Saudiyya a dukkan majalisun masarautar Saudiyya.

A matakin jama'a, Bundagji ta kasance mai taka rawa wajen samar da sha'awar mata na tsayawa takara a zaɓukan ƙananan hukumomin da ba na dimokuradiyya ba.[3] A shekarar 2004, ita ce mace ta farko a yankin Yamma da ta bayyana sha'awarta ta tsayawa takara.[4] A shekara ta 2009 ta kafa ƙungiyar (Balady Initiative) mai fafutukar kare hakkin mata a matsayin shugabar kasa a ofishin gwamnati. Ita ce wacce ta kafa ƙungiyar MUWATANA mai fafutukar ci gaban gari ta hanyar mai da hankali kan mutum, wuri da bin doka da oda.[2]

Manazarta gyara sashe

  1. "ﻨﻅﺭﺓ ﻋﺎﻤﺔ". Archived from the original on 2013-09-18. Retrieved 2013-09-28.
  2. 2.0 2.1 "Jeddah's Who's Who Fatin Bundagji: A Lady With A Message". Archived from the original on 2013-09-28.
  3. What if Saudi Arabia Threw an Election for Women and Nobody Came? Foreign Policy
  4. "3 Women Nominate Themselves for Municipal Elections". Arab News