Port Harcourt

Fatakwal
(an turo daga Fatakwal)

Port Harcourt Birni ne, da ke a jihar Rivers, a kasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Rivers. Port harcourt ita ce birni na biyar a girma, bayan Lagos, Kano, Ibadan da Kaduna.[1][2] Bisa ga kidayar jama'a a shekarar 2006, akwai kimanin mutane 1,382,592,[3] amma an hakayo cewa akwai kimanin mutane miliyan 1,865,000 ke zaune a babban birnin. Turawan mulkin mallaka suka gina tashan jirgin ruwa a garin don daukan gawayi daga Enugu wanda ke da nisan kilomita 243 kilometres (151 mi) zuwa kasashensu na ketare, da kuma titin jirgin kasa da turawan suna gina wanda ya hade garuruwan biyu wanda ake kira da "Eastern Line".[4][5]

Port Harcourt


Suna saboda Lewis Harcourt, 1st Viscount Harcourt (en) Fassara
Wuri
Map
 4°45′N 7°00′E / 4.75°N 7°E / 4.75; 7
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
Jihohin NajeriyaJihar rivers
Ƙananan hukumumin a NijeriyaPort Harcourt (karamar hukuma)
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 3,325,000 (2022)
• Yawan mutane 9,236.11 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Bangare na South South (en) Fassara
Yawan fili 360 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Guinea
Altitude (en) Fassara 18 m-18
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1912
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 500101 to 500272
Kasancewa a yanki na lokaci
Tsarin lamba ta kiran tarho +234
Port-Harcourt.
Air Force junction Port Harcourt
filin wasa a PORT Harcourt

Kafin shekara ta 1912, wurin da ake kira Port harcourt garine na mutanen Ikwerre da Ogbulom.

Tattalin arzikin Port harcourt ya koma harkokin man fetur a yayinda aka fara fitar da mai ta jihar a shekara ta 1958. Ta hanyar gajiyar da Birnin Port harcourt ta samu daga Kamfononin man fetur na Najeriya, birnin ta samu bunkasa zuwa tsarukan gine-gine na zamani iri iri.[6]

Asali suna

gyara sashe

An samar da garin a cikin shekarar 1912, amma ba'a sanya mata suna ba har zuwa watan Augustan 1913. A lokacin da shugaban Najeriya, Gwamna Sir Fedrick Lord Lugard ya sanya mata suna "Port Harcourt" don karramawa ga Lewis Vernon Harcourt sakataren Gwamnati na wannan yankunan mallakar turawa a lokacin.[7] Ma'anan kalmar a harshen Okrika ita ce Hakoti Kiri ko kuma Parakot. Sunan garin da harshen Obulom shi ne Obomotu, wanda ke nufin babban gida

Shugaban Najeriya kuma shugaban yankin kudancin Najeriya Lord Lugard ya kirkiri Birnin Port Harcourt a shekara ta 1912. Manufar samar da wannan tasha shi ne don sufurin gawayi da aka gano a Enugu zuwa ketare. Gwamnatin mulkin mallaka ta tilasta ainihin mutanen garin (Diobu) su bar wurin, haka ginin tashar jirgin ruwan ya fara a shekarar 1912. Sauran garuruwa da aka haɗe don fadada garin sun hada da Oroworukwo, Nkpogu, da kuma Rumuomasi. An yi amfani da yankin Port Harcourt a matsayin tushen yaki don yakar German Cameroon. Bayan gano man fetur a Oloibiri a shekara ta 1956, ta Port harcourt aka fara fitar da man-fetur din a shekara ta 1958. Port harcourt ta zamo cibiyar kasuwancin man fetur a Najeriya. Kuma tabbas ta sama gajiyar wannan alaka saboda ta samu bunƙasa da ci gaba a fannoni daban daban na zamani.

Har wayau ci gaban garin ya hada da zamantowar ta cibiyar kamfanonin kere-kere na kungiyar Eastern region na lokacin; matsayin ta a Niger Delta da kuma a matsayin cibiyar al'adu da kuma muhimmancin ta ga mutanen jihar Rivers.

Bayan an ci jamhuriyar Biafra da yaki a shekarar 1967, Port Harcourt ta fada karkashin mulkin gwamnatin Najeria a ranar 19 ga watan Mayun 1978.

Labarin kasa

gyara sashe

Asalin birnin Port Harcourt shi ne daidai gabar da tashar jiragen ruwa take a karkashin karamar hukumar Port Harcourt da ke Jihar Rivers. Birnin ya hada da karamar hukumar Port Harcourt din ita kanta da kuma sauran wurare kamar Obio-Akpor da Eleme. Yankin Portharcourt ya kunshi kananan hukumomi guda takwas wanda suka hada da Port Harcourt, Okrika, Obio-Akpor, Ikwerre, Oyigbo, Ogu–Bolo, Etche and Eleme. Akwai cunkoson al'umma a Port harcourt wacce karamar hukumace ta Jihar Rivers kuma kasance ita kadai ce babban birni a garin. An ayyana yawan jama'ar birnin kimanin mutum miliyan biyu a shekara ta 2009, saboda haka ta zamanto ɗaya daga cikin birane nafi girma (a yawan jama'a) a Najeriya.

Port Harcourt na da yanayi na Tropical Wet Climate da damuna mai tsawo da ruwa mai karfi, sannan akwai rani mara tsawo. Watanni tsakanin watan Disamba zuwa watan Fabrairu ne kadai ke da yanayi na rani a garin. Sannan akwai karancin lokacin sanyi a birni. Watan da aka fi ruwan sama a garin shi ne watan Satumba da kimanin (367mm) na ruwan sama. Watan Disamba shi ne wata da ya fi kowanne karancin ruwan sama da kimanin (20mm). Yanayi na zafi/sanyi yana daidaita a duka shekara, yawanci tsakanin 25 °C-28 °C a birnin.

Climate data for Port Harcourt
Watan Janairu Fabrairu Maris Afrilu Mayu Yuni Yuli Ogusta Satumba Oktoba Nuwamba Disamba Shekara
Average high °C (°F) 32.4
(90.3)
33.4
(92.1)
32.6
(90.7)
32.1
(89.8)
31.2
(88.2)
30.0
(86.0)
28.8
(83.8)
28.7
(83.7)
29.3
(84.7)
30.2
(86.4)
31.3
(88.3)
31.8
(89.2)
31.0
(87.8)
Average low °C (°F) 21.2
(70.2)
22.5
(72.5)
23.3
(73.9)
23.2
(73.8)
23.2
(73.8)
22.7
(72.9)
22.4
(72.3)
22.4
(72.3)
22.4
(72.3)
22.4
(72.3)
22.4
(72.3)
21.4
(70.5)
22.5
(72.5)
Average rainfall mm (inches) 22.2
(0.87)
56.5
(2.22)
116.3
(4.58)
183.6
(7.23)
222.7
(8.77)
273.3
(10.76)
356.5
(14.04)
326.8
(12.87)
367.1
(14.45)
263.1
(10.36)
96.9
(3.81)
25.9
(1.02)
2,310.9
(90.98)
Average rainy days 2.2 4.6 8.6 11.6 14.2 16.5 19.7 19.8 20.1 14.4 5.9 2.1 139.7
Average relative humidity (%) (at 15:00 LST) 54.6 57.0 65.3 70.1 74.1 78.5 81.1 81.6 81.3 77.7 69.3 58.5 70.8
Mean monthly sunshine hours 142.6 123.2 114.7 132.0 139.5 102.0 77.5 74.4 78.0 102.3 132.0 148.8 1,367
Mean daily sunshine hours 4.6 4.4 3.7 4.4 4.5 3.4 2.5 2.4 2.6 3.3 4.4 4.8 3.7
Source 1: World Meteorological Organization[8]
Source 2: NOAA (sun and relative humidity, 1961–1990)[9]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Population of Cities in Nigeria (2021)". worldpopulationreview.com. Retrieved 19 November 2021.
  2. "Nigeria: cities with the largest population 2021". Statista. Retrieved 19 November 2021.
  3. "Arizona-Ogwu, L.Chinedu (16 February 2011). "Port Harcourt PDP Rally Stampede: Irregular Or Deregulated Police Action?". Nigerians In America. Archived from the original on 25 June 2014. Retrieved 25 June 2014.
  4. Port Harcourt, Nigeria Metro Area Population 1950-2021". www.macrotrends.net. Retrieved 19 November2021.
  5. "Udo, Reuben K. (1970). Geographical Regions of Nigeria. University of California Press. p. 85.
  6. "Hudgens, Jim; Trillo, Richard (2003). The rough guide to West Africa (4 ed.). Rough Guides. p. 1075. ISBN 1-843-53118-6.
  7. "Okafor, S.O. (January 1973). "The Port Harcourt Issue: A Note on Dr Tamuno's Article". African Affairs. Royal African Society. Oxford University Press. 72 (286): 74. doi:10.1093/oxfordjournals.afraf.a096323.
  8. "World Weather Information Service – Port Harcourt". World Meteorological Organization. Archived from the original on 17 August 2016. Retrieved 7 July 2016.
  9. "Port Harcourt Climate Normals 1961–1990". National Oceanic and Atmospheric Administration. Retrieved 7 July 2016.