Farida Usman Ajebo jaruma ce Kuma mai bada umarni sannan mai shirya fim ce a masana antar fim ta Hausa wato kannywood ta biyo jaruma [1]muhibbat Abdussalam. Farida ba bakuwa bace a masana antar ta Dade tana Bada gudummawar ta a harkan.daga baya ta koma waka.[2]

Takaitaccen Tarihin Ta

gyara sashe

Cikakken sunan ta shine Farida Usman bafullatana daga jihar Adamawa Amma anfi sanin ta da Farida Ajebo, darakta ce jaruma furodusa sannan mawaƙiya a Masana antar. Mace ce Mai Hali Mai ladabi da biyayya a masana antar kowa na yabon halayenn haife ta a garin sokoto aiki yakai baban ta can aka haifeta daga baya suka dawo garin Abuja acan ta girma , bayan rasuwar kakanta suka dawo jihar kaduna daga Nan take amsa sunan ta a matsayin yar jihar.Ta samo suna Ajebo ne daga mahaifin ta lokacin kanwarta ta na makarantar"police academy" ana kiran ta da skellegaga SE ake tambayan ta me sunan ke nufi shine tace ai ita tana son sunan. To shine baban su yace ita Kuma Farida yar shi itace Ajebo to tun daga Nan sunan yabi ta

Farida tayi karatun firamare a "Jibril memorial" tayi karatun sakandiri a "karu secondary school" daga Nan ta shiga "shehu Idris college of health Makarfi" inda tai karatun ND da Kuma HND acan.

Ta fara Waka ne saboda tana son waka, tun tana sakandiri take shiga Hausa club suke yin Waka in za,ai taro. Bayan ta gama ne ta hadu da wasu suka ce suna da sitediyon Waka shine ita tace tana so tayi. Ta fara Waka da wakar Siyasa. Ita ke rubuta wakar da kanta.

Wakokin ta;

  • in dai da tunani
  • Mai kunya
  • ki Soni
  • Matan gida
  • Da so muka saba

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-07-30. Retrieved 2023-07-30.
  2. https://fimmagazine.com/yadda-na-soma-zama-darakta-mawa%C6%99iyar-kannywood-farida-ajebo/