Emmanuel Ndubisi Maduagwu (an haife shi a shekara ta 1947) jami'ar Ibadan ta ba shi muƙamin farfesa a sashen nazarin kimiyyar halittu a shekarar 1989 kuma ya yi hidima a jami'ar har zuwa watan Disamba 2013.[1] Ya kasance Farfesa na Biochemistry na kwangila a Jami'ar Covenant. Shi fellow ne na Cibiyar Nazarin Kimiyya ta Najeriya kuma an zaɓe shi cikin Ƙungiyar Kwalejin a Babban Taronta na Shekara-shekara da aka gudanar a cikin watan Janairu 2015.[2] Farfesa Mashawarci ne a fannin kare lafiyar abinci da ilimin guba na abinci. A halin yanzu Farfesa Maduagwu Farfesa ne kuma Shugaban Sashen Kimiyyar Halittu na Jami’ar Chrisland da ke Abeokuta a Najeriya.

Emmanuel Ndubisi Maduagwu
Rayuwa
Haihuwa 1947 (77/78 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar Ibadan
Sana'a
Sana'a chemist (en) Fassara da Malami
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Maduagwu ya halarci makarantar Dennis Memorial Grammar School, Onitsha Archived 2023-12-14 at the Wayback Machine, Jihar Anambra, Najeriya inda ya sami takardar shaidar makarantar Cambridge ta yammacin Afirka a shekarar 1962 da kuma takardar shaidar sakandare ta Cambridge a shekarar 1964.

Ya sami digirinsa da digirin digirgir a fannin kimiyyar halittu daga Jami'ar Ibadan a shekarar 1972 da 1976. Ya shiga sashen nazarin kimiyyar halittu, kwalejin likitanci ta Jami’ar Ibadan, a matsayin malami mai daraja ta biyu a shekarar 1978 kuma an naɗa shi babban malami a shekarar 1981.[3] A shekarar 1989, ya zama cikakken farfesa a fannin kimiyyar halittu a wannan jami'a. Ya yi ritaya daga hidimar jami’ar Ibadan a shekarar 2012, bayan da ya kai shekaru 65 na dole ya yi ritaya.[4]

Fellowships

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. "Nigerian chemists famous people". Famous Scientists (in Turanci). 2020-03-31. Retrieved 2020-05-24.
  2. "NAS holds public lecture induction of fellows". nas.org.ng. Archived from the original on July 8, 2015. Retrieved July 13, 2015.
  3. "Staff - Department of Biochemistry, College of Medicine, University". University of Ibadan. Archived from the original on March 4, 2016. Retrieved July 14, 2015.
  4. "Professor Emmanuel Maduagwu". covenantuniversity.edu.ng. Archived from the original on July 14, 2015. Retrieved July 14, 2015.