Emeka Chinedu
Emeka Martins Chinedu ɗan siyasan Najeriya ne. A halin yanzu mamba ne mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ahiazu Mbaise/Ezinihitte a majalisar wakilai. [1] [2]
Emeka Chinedu | |||
---|---|---|---|
11 ga Yuni, 2019 - District: Ahiazu Mbaise/Ezinihitte | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 2 ga Faburairu, 1965 (59 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Emeka Martins Chinedu a ranar 2 ga watan Fabrairun 1965. [2]
Aikin siyasa
gyara sasheA zaɓen majalisar wakilai na shekarar 2023, ya sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) don sake lashe zaɓen karo na biyu a matsayin mamba mai wakiltar mazaɓar tarayya ta Ahiazu Mbaise/Ezinihitte. [3] [4] Ya zuwa ranar 5 ga watan Disamba, 2024, ya ɗauki nauyin kudirori huɗu wadanda suka tsallake karatu na farko a majalisar dokokin ƙasar. [5] A halin yanzu yana aiki a matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar wakilai a babban birnin tarayya (FCT). [6]
Kalubale na shari'a da nasara
gyara sasheA ranar 7 ga watan Satumba, 2023, wata kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Legas ta tabbatar da nasarar Emeka Chinedu a zaɓen, inda ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar Darlington Amaechi na jam’iyyar Labour (LP) da Nnanna Igbokwe na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), bisa dalilan cewa ba ta samu ba cancanta da hukumci. [7] [8] Tun da farko a shekarar 2019, kotun sauraron ƙararrakin zaɓe da ke zama a Owerri ta yi watsi da ƙarar da Nnanna Igbokwe na jam’iyyar APC ya shigar kan Emeka Chinedu a zaɓen mazaɓar tarayya na Ezinihitte Mbaise/Ahiazu Mbaise, bisa dalilan da ya sa bai cancanta ba. [9]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "National Assembly | Federal Republic of Nigeria". nass.gov.ng. Retrieved 2024-12-12.
- ↑ 2.0 2.1 "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 2024-12-12. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ "Citizen Science Nigeria". citizensciencenigeria.org (in Turanci). Retrieved 2024-12-12.
- ↑ olufemiajasa (2023-11-05). "Appeal Court affirms election of Chinedu as Imo PDP Rep". Vanguard News (in Turanci). Retrieved 2024-12-12.
- ↑ "Hon. Emeka Chinedu Pushes Four Key Bills Through First Reading" (in Turanci). 2024-12-06. Retrieved 2024-12-12.
- ↑ "Hon. Emeka Chinedu: Honouring A Visionary Leader's Birthday" (in Turanci). 2024-02-02. Retrieved 2024-12-12.
- ↑ TheCable (2023-11-04). "Appeal court affirms Emeka Chinedu winner of Imo reps seat". TheCable (in Turanci). Retrieved 2024-12-12.
- ↑ "Reps Seat: Appeal Court Declares Venue Of Imo PDP Primaries Valid, Affirms Emeka Chinedu's Election – THISDAYLIVE". ThisDay. Retrieved 2024-12-12.
- ↑ "Imo: Tribunal dismisses petition against Reps member - Daily Trust". Daily Trust (in Turanci). 2019-09-04. Retrieved 2024-12-12.