Elizabeth Anionwu
Elizabeth Nneka Anionwu DBE FRCN (an haife ta Elizabeth Mary Furlong; 2 ga Yuli 1947) ma'aikaciyar jinya ce 'yar kasar Ingila, mai kula da lafiya, malama ce, kuma Emeritus farfesa a fannin jinya a Jami'ar West London.
Elizabeth Anionwu | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Elizabeth Mary Furlong | ||
Haihuwa | Birmingham, 2 ga Yuli, 1947 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | nurse (en) | ||
Employers |
London School of Hygiene & Tropical Medicine (en) Jami'ar Yammacin London | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
Mamba | Black Female Professors Forum (en) | ||
elizabethanionwu.co.uk |
Tarihi
gyara sasheElizabeth Nneka Anionwu an haife ta ne Elizabeth Mary Furlong a Birmingham, Ingila, ga mahaifiya ‘yar kasar Ireland kuma mahaifin dan Najeriya. Mahaifiyarta, Mary Maureen Furlong, tana shekararta ta biyu tana karatun Karatu a Kwalejin Newnham, Jami'ar Cambridge. Mahaifinta, Lawrence Odiatu Victor Anionwu, yana karatun lauya a Jami'ar Cambridge.
Aiki
gyara sasheAnionwu ta fara aikinta na jinya tun tana ƙarama bayan tasirantuwa da wata mata mai zaman zuhudun kiristanci da ke kula da marasa lafiya A lokacin da take da shekaru 16, ta bar makaranta a matakan O-level kuma ta fara aiki a matsayin mataimakiyar aikin jinya a makaranta ta Wolverhampton. Daga baya, ta ci gaba da karatun ta don zama ma'aikaciyar jinya da kuma mai koyarwa. Ta yi tafiya zuwa Amurka don yin karatun bad shawara ga cibiyoyin kula da masu sikila da thalassaemia saboda ba a samun kwasa-kwasan a Burtaniya a lokacin.
Manazarta
gyara sashehttps://guardian.ng/saturday-magazine/prof-elizabeth-nneka-anionwu-from-humble-background-to-pinnacle-of-nursing-sickle-cell-expertise/ Archived 2019-03-29 at the Wayback Machine
http://www.uwl.ac.uk/academic-schools/nursing-midwifery/professor-dame-elizabeth-anionwu Archived 2017-12-10 at the Wayback Machine