Eli Mwanang'onze
Dr Elimelek Hanakumbo Bulowa Mwanang'onze kwararren Malami ne a fannin ilimi ɗan ƙasar Zambia kuma tsohon ɗan siyasa. Ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Dokoki ta ƙasa mai wakiltar Bweengwa daga shekarun 1988 har zuwa 1991,[1] da kuma riƙe muƙamin Ministan Ilimi, Matasa da Wasanni. [2]
Eli Mwanang'onze | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Zambiya | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Manitoba (en) | ||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Malami | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | United National Independence Party (en) |
Tarihin Rayuwa
gyara sasheMwanang'onze ya sami MSc a fannin ilimin ƙasa a Jami'ar Manitoba a shekara ta 1974, kafin ya sami digiri na uku a jami'a guda a shekarar 1978. Daga baya ya yi aiki a matsayin malami a Makarantar Mines a Jami'ar Zambiya, [3] kuma ya kasance shugaban kwamitin edita na Journal of African Marxists. [4] Daga baya ya zama ma'aikacin gwamnati kuma ya kasance babban sakataren ma'adinai. [5]
An zaɓi Mwanang'onze a matsayin ɗan majalisar dokokin ƙasar ne a babban zaɓen ƙasar na shekarar 1988 a daidai lokacin da ƙasar Zambiya ta kasance ƙasa mai jam'iyya ɗaya da jam'iyyar 'yancin kai ta United National Independence Party a matsayin jam'iyyar doka tilo.[6] Lokacin da aka ɓullo da tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da yawa a farkon shekarun 1990, bai tsaya takara a babban zaɓen shekara ta 1991 ba kuma Baldwin Nkumbula ya gaje shi. [7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Debates- Friday, 21st October, 2011". National Assembly of Zambia. Retrieved 9 February 2020.
- ↑ World Conference on Education for All UNESCO
- ↑ Yong Zhou (2013) The Development Potential of Precambrian Mineral Deposits: Natural Resources and Energy Division, U.N. Department of Technical Co-Operation for Development, Elsevier, p427
- ↑ Journal of African Marxists Ufahamu: A Journal of African Studies
- ↑ "Low copper prices threaten nation's mining future", Times of Zambia, 9 September 1982
- ↑ Yong Zhou (2013) The Development Potential of Precambrian Mineral Deposits: Natural Resources and Energy Division, U.N. Department of Technical Co-Operation for Development, Elsevier, p427
- ↑ Zambia Election Passport