Ebere Orji
Ebere Orji (an haife ta a ranar 23 ga watan Disamba a shekara ta 1992) 'yar wasan ƙwallon ƙafa ce ta ƙasar Najeriya a halin yanzu tana taka leda a Sundsvall DFF a Elitettan Sweden.[1] Ta taba taka leda a kungiyoyi da yawa a Najeriya, Sweden da Hungary amma musamman tayi wasa Ferencváros a Női NB I na Hungary da Rivers angels a cikin ƙasarta a gasar Premier ta Mata ta Najeriya. Ta kuma wakilci Najeriya a matakin ƙasa da ƙasa a matsayin ƙungiyar a gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA a shekarar 2011, da kuma gasar cin kofin duniya na 'yan ƙasa da shekara 20 da 'yan ƙasa da shekaru 17.[2]
Ebere Orji | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Enugu, 23 Disamba 1992 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Ataka | ||||||||||||||||||||||
Tsayi | 166 cm |
Aikin kulob/ƙungiya
gyara sasheTare da Rivers angels, ta taba zira kwallaye uku hat-trick a kulob ɗin COD United Ladies a nasarar 6-1 akan hanyarsu ta ƙarshe ta lashe gasar cin kofin Federation a shekara ta 2014.[3]
A cikin shekarar 2015 tare da Ferencváros, ta lashe gasar zakarun Hungary (Női NB I) da Kofin Hungarian. A cikin kakar 2016 zuwa 2017, Orji ta ƙare a matsayin wanda ta fi zira kwallaye a Női NB I da kwallaye 27.[4]
A cikin shekarar 2019 Orji ta kuma lashe kambin Elitettan tare da Umeå IK, inda ta zira kwallaye 11 a wasannin gasar 26.[5]
Ayyukan kasa
gyara sasheA lokacin da take da shekaru 15, Orji ta fara buga wasanta na farko a duniya ga mata 'yan Najeriya 'yan ƙasa da shekaru 17 a gasar cin kofin duniya na mata na 'yan ƙasa da shekaru 17 a shekara ta 2008 a wasan da suka doke Koriya ta Kudu da ci 2-1 a matakin rukuni. Orji ta ci kwallonta ta farko ta ƙasa da ƙasa a 'yan kasa da shekaru a gasar daya tak a wasan da suka tashi 2–2 da Brazil. Kwanaki 17 bayan Brazil, ta korosu a gasar Orji ta sake wakiltar Najeriya, a wannan karon a matakin kasa da 20 a gasar cin kofin duniya ta mata 'yan kasa da shekaru 20 na shekarar 2008.[6] Orji ta zura kwallo a wasanta na farko a kungiyar a wasan da suka tashi 1-1 da Ingila sannan kuma ta ƙara zura kwallaye biyu yayin da Falconets ta yi waje da ita a wasan daf da na kusa da karshe a hannun Faransa da ci 2-3.[7]
Shekaru biyu bayan haka, an sake kiran Orji zuwa tawagar 'yan kasa na shekara 20 a gasar cin kofin duniya ta mata ta U-20 na shekarar 2010 kuma ta sami babban nasara a cikin tawagar da ta fitar da zakarun Amurka a wasan kusa da na ƙarshe kuma a ƙarshe ta kai wasan ƙarshe na gasar cin kofin duniya.[9] Gasar da aka yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Jamus mai masaukin baki. Orji ta taba kasancewa a kungiyar kuma ta zura kwallaye biyu a gasar, sau ɗaya ne kaɗai kwallo daya tilo a wasan da Najeriya ta doke Colombia.
Orji ta fara bugawa Najeriya wasa a wasan sada zumunta da Jamus, amma bayan mintuna 29 aka sauya ta, sannan Najeriya ta sha kashi da ci 8-0.
Orji na cikin tawagar 'yan wasan Najeriya da suka lashe gasar cin kofin Afirka ta mata a shekarar 2010. Ta kuma fitowa a gasar cin kofin matan Afirka ta shekarar 2012.[10]
Ta fara wasa a gasar cin kofin duniya ta zo a gasar cin kofin duniya ta mata na shekara ta 2011, wanda ta fara a duk wasanni uku na rukuni. Najeriya ta ƙasa tsallakewa zuwa matakin rukuni na gaba.[11]
A cikin shekarar 2012, Orji ta sake wakiltan 'yan kasa da shekaru 20 a gasar cin kofin duniya na mata na U-20 na shekarar 2012, ta bayyana a matsayin mai maye gurbi a duk wasannin Najeriya har sai da Amurka ta fitar da su a wasan kusa da na karshe. Orji ta buga wasanni 15 a Najeriya ‘yan ƙasa da shekara 20 tsakanin shekara ta 2008 zuwa 2012, inda ta ci kwallaye 5.[12]
Girmamawa
gyara sasheKulob/ƙungiya
gyara sashe- Delta Queens
- Gasar Premier Matan Najeriya : Wanda ya lashe 2009
- Kofin Aiteo : Wanda ya ci 2009
- Rivers Angels
- Gasar Premier Matan Najeriya : Wanda ya lashe gasar a shekara ta 2010 zuwa 2014
- Kofin Aiteo : Wanda ya ci a shekara ta 2010, da shekara ta 2011, da kuma shekara ta 2012
- Ferencváros
- Női NB I : Nasara 2015zuwa 2016
- Női NB I : Wanda ya zo na biyu 2016zuwa 2017
- Nöi Magyar Kupa: Nasara 2015 zuwa 2016 da kuma 2017
- Imea IK
- Elitettan : Mai nasara 2019
Ƙasashen Duniya
gyara sashe- Najeriya U-20
- Gasar cin kofin duniya ta mata ta U-20 : ta zo na biyu a shekara ta 2010
- Najeriya
- Gasar Cin Kofin Mata ta Afirka : Wanda ya ci nasara a shekara ta 2010
Manazarta
gyara sashe- ↑ Falcons not scared of Germany–Ebere Orji–Vanguard News". Vanguard News. 23 June 2011. Retrieved 7 December 2014.
- ↑ Ebere Orji: Ebere Orji: Umea IK". www.playmakerstats.com. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ Rivers Angels Lift FA Cup With Falcons Players–The Newswriter". Retrieved 3 November 2019.
- ↑ A Női Labdarúgó Bajnokságok oldala". www.noilabdarugas.hu. Retrieved 31 October 2019.
- ↑ Players– Elitettan–Sweden–Results, fixtures, tables and news–Soccerway". us.soccerway.com. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ Previous Tournaments". FIFA.com. Archived from the original on 29 October 2013. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ FIFA U-20 Women's WC Chile 2008–Matches–Nigeria-France". FIFA.com. Archived from the original on 9 March 2016. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ "Nigeria stars reflect on U-17 introduction". FIFA.com (in Turanci). 21 September 2016. Archived from the original on 3 November 2019. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ "FIFA U-20 Women's World Cup 2010–News–Germany triumph on home turf–FIFA.com". www.fifa.com. Archived from the original on 3 November 2019.
- ↑ Germany–Nigeria 8:0 (Women Friendlies 2010, November)". worldfootball.net. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ (PDF). 28 September 2012 https://web.archive.org/ web/20120928064407/http://www.cafonline.com/ userfiles/file/Comp/AWC2010/ List_Players_AWC2010.pdf. Archived from the original (PDF) on 28 September 2012. Retrieved 3 November 2019.
- ↑ (PDF). 22 February 2013 https://web.archive.org/ web/20130222184107/http://www.cafonline.com/ userfiles/file/Comp/AWC2013/List_of_players.pdf. Archived from the original (PDF) on 22 February 2013. Retrieved 3 November 2019.
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Ebere Orji – FIFA competition record
- Ebere Orji at Soccerway
- Goal.com profile