Dipo Dina
Otunba Dipo Dina (an haifeshi ranar 15 ga watan Yuli, 1960 - Janairu 25, 2010) ɗan siyasan Najeriya ne, mai taimakon jama'a, mai gudanarwa, jagoran al'umma kuma akawu daga jihar Ogun.
Dipo Dina | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ijebu Ode, 15 ga Yuli, 1960 |
Mutuwa | 25 ga Janairu, 2010 |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar jahar Lagos |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da philanthropist (en) |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | Action Congress of Nigeria |
Rayuwar farko da aiki
gyara sasheAdedipupo Akanni Dina. An haife shi ranar 15 ga watan Yuli, 1960, cikin dangin Dipo Alapo Ekun na Iyanro, Ijebu Ode, jihar Ogun. Ya yi karatunsa na sakandare a Baptist Academy, Legas, kafin ya wuce Jami'ar Legas inda ya sami digiri na farko a fannin Accounting sannan ya sami digiri na biyu, M.Sc. a fannin; kuɗi-(finance).
Ya zama, Chartered Accountant a 1984 kuma daga baya ya kafa, kuma Babban Abokin Hulɗa a Dele Dina & Co. (kamfanin lissafin kuɗi) har zuwa mutuwarsa. A tsakanin shekarar 1997 zuwa 1999 Dipo ya riƙe muƙamin shugaban hukumar sayan manyan kayayyaki ta jihar Ogun inda rahotanni suka ce ya bayar da gudummawar albashi da alawus dinsa ga makarantar naƙasassu da ke Ijebu Ode.[1]
Tarihin Siyasa
gyara sasheDipo ya tsunduma cikin harkokin siyasa a shekarar 2003, kuma ya zama ɗan takarar gwamnan jihar Ogun a zaɓen 2007 bayan ya koma rusheshiyar jam’iyyar Action Congress (AC) kafin ta rushe.[2] An bayyana cewa yana baiwa ɗalibai kusan 400 tallafin kuɗi a jihar duk shekara, kuma a lokacin yaƙin neman zaɓen sa na gwamna a shekarar 2007, an baiwa makarantun firamare da sakandire da manyan makarantun jihar kimanin lita miliyan huɗu na motsa jiki kyauta. Ya kafa kungiyar ‘Ogunnet’, ƙungiya mai zaman kanta, domin aiwatar da shirye-shiryensa na siyasa.[3]
Mutuwa
gyara sasheA ranar 25 ga Janairu, 2010, a kan hanyarsa ta zuwa gidansa da ke Dolphin Estate, Ikoyi, an sace Dina Dipo a wata mota zuwa wurin da ba a sani ba, inda aka kashe shi.[4][5][6][7] Rahotanni sun ce maharin ya tsira da ran wasu fasinjoji biyu ciki har da direbansa.[8]
Tunawa
gyara sasheAn saka sunan sa a Babban filin wasa na Otunba Dipo Dina International Stadium, dake Ijebu-Ode don karrama shi, da tsohon gwamna Ibikunle Amosun yayi.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Kehinde, Akinyemi (Jan 30, 2010). "Dipo Dina: Dream shattered by bullet". Daily Trust. Archived from the original on 20 July 2020. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ John A. A. Ayoade, Adeoye A. Akinsanya (2013). Nigeria's critical elections. Rowman & Littlefield. pp. 241, 242. ISBN 9780739175880. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ Musa, Odoshimokhe. "Dina left outstanding legacy, says Obadara". The Nation. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ Ayo, Bada. "Remembering Dipo Dina, 10 Years After". Independent NG. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ Don Prince Victor Ovrawah (14 March 2012). Catastrophic Revelations. ISBN 9781469142388. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ Ayodeji Olukoju, Olutayo Adesina, Abimbola Adesoji (15 January 2019). Security Challenges and Management in Modern Nigeria. Rowman & Littlefield. p. 272. ISBN 9781527525573.
- ↑ Ifeoha, Azikiwe (2013). Nigeria,echoes of a century:1999-2014. AuthorHouse. ISBN 9781481729277. Retrieved 20 July 2020.
- ↑ Kolade, Larewaju. "Who killed Dipo?". The Vanguard. Retrieved 20 July 2020.