Dibiagwu Eugene Okechukwu
Dibiagwu Eugene Okechukwu ɗan siyasan Najeriya ne. A yanzu haka mamba ne mai wakiltar mazaɓar Ohaji/Egbema/Oguta/Oru ta Yamma a majalisar wakilai. [1]
Dibiagwu Eugene Okechukwu | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Dibiagwu Eugene Okechukwu a ranar 24 ga watan Disamba 1971. [2]
Aikin siyasa
gyara sasheEugene dai ya gaji Uju Kingsley Chima ne bayan ya tsaya takara a zaɓen ‘yan majalisar wakilai na shekarar 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar APC kuma ya samu nasara inda ya doke takwarorinsa na jam’iyyun adawa. [3] [1] A wani ɓangare na tallafi da karfafawa, ya raba wa manoman mazaɓar sa iri na shuka don ƙara yawan abinci. [4]
Ƙalubale na shari'a da nasara
gyara sasheKotun sauraren kararrakin zaɓe ta jihar Imo da ke zamanta a jihar Nasarawa ta tabbatar da nasarar Eugene Okechukwu a zaɓen shekarar 2023, inda daga karshe ta yi watsi da ƙarar da abokin takararsa Ilo Ezenwa Collins na jam'iyyar Labour (LP) ya shigar bisa dalilin cewa ba ta cancanta ba. . [5]
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 ""You All Will Be Proud That You Hired Me As Your Reps. Member", Hon Dibiagwu Assure Constituents". www.thenigerianvoice.com. Retrieved 2024-12-14. Cite error: Invalid
<ref>
tag; name ":0" defined multiple times with different content - ↑ "10th National Assembly Members - Voter - Validating the Office of the Electorate on Representation". orderpaper.ng. Retrieved 2024-12-14.
- ↑ "2023 Imo state house of representatives election results - eduweb" (in Turanci). Retrieved 2024-12-16.
- ↑ "Food Production: Dibiagwu Empowers 150 Constituents With Improved Agricultural Seedlings". Pressman. 29 July 2023. Retrieved 16 December 2024.
- ↑ Tsa, Godwin (7 September 2023). "Imo House of Reps seat: Tribunal declares Dibiagwu Okechukwu winner". The Sun Nigeria. Retrieved 16 December 2024.