[1]David Ospina Ramírez (an haifeshi a ranar 31 ga watan Ogusta shekarar alif 1988), ya kasance kwararren dan wasan ƙasar Kolambiya ne wanda ke taka leda Categorian Primera kungiyar kwallon kafa ta Atletico Nacional d kuma kungiyar kwallon kafa Kolambiya wayo kungiyar ƙasa.

David Ospina
Rayuwa
Cikakken suna David Ospina Ramírez
Haihuwa Medellín, 31 ga Augusta, 1988 (36 shekaru)
ƙasa Kolombiya
Faransa
Ƴan uwa
Ahali Daniela Ospina (en) Fassara
Karatu
Harsuna Yaren Sifen
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
Atlético Nacional (en) Fassara2004-2008970
  Colombia national under-20 football team (en) Fassara2005-2007120
  Colombia men's national football team (en) Fassara2007-
  San Lorenzo de Almagro (en) Fassara2008-20141890
Arsenal FC27 ga Yuli, 2014-4 ga Yuli, 2019700
  SSC Napoli (en) Fassara17 ga Augusta, 2018-30 Mayu 2019170
  SSC Napoli (en) Fassara4 ga Yuli, 2019-30 ga Yuni, 2022
Al-Nassrga Yuli, 2022-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai tsaran raga
Lamban wasa 25
Nauyi 76 kg
Tsayi 183 cm
David Ospina
David Ospina
Dabid Ospina

Dan wasan ya fara yin kungiyar Atletico Nacional inda ya fara taka leda a ƙungiyar tun shekarar alif 2005. Bayan lashe gasar lig da yayi har sau biyu tare da kungiyar kwallon kafa ta Vardolagas, mai tsaron ya koma taka leda lig1 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nice. Bayan nan kuma ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal a shekarar alif 2014. Inda ya rattaba hannu na tsawon kwantiragin shekaru 4. A lokacin da yake garin Landan, dan wasan ya samu nasarar lashe Kofi har guda ukku a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal inda ya lashe gasar kofin FA a shekarar alif 2015 da kuma gasar kofin FA din na biyu a shekarar alif 2017, sai kuma gasar farantin Community Shield a shekarar alif 2017.

A shekarar alif 2018 dan wasan yaje zaman aro a kungiyar kwallon kafa ta Napoli amma a shekara ta gaba suka kulla yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal akan dan wasan inda ya koma zama na dindindin. A shekarar alif 2020, mai tsaron ragar ya taka rawar gani sosai a gasar Coppa Italiya da suka buga a shekarar. Sai dai kuma biyo bayan rashin nasara da akayi na rashin daidaito wajan kwantiragin ɗan wasan, hakan yasa ya koma buga gasar saudi Pro League a kungiyar kwallon kafa ta Alnassr wadda ke kasar Saudiyya a shekarar alif 2022.

A fannin kasa kuma, dan wasan ya wakilci kasar tashi ta haihuwa wato Kwalambiya. Mai tsaron ragar ya fara wakiltar kasar tashi tun shekarar alif 2007. Lokacin da yake dan saurayi ya wakilci kasar tashi a gasar kofin duniya na matasa wato FIFA World Championship na matasa wanda aka buga a shekarar alif 2005. Kuma yana daya daga cikin jerin yan wasan da suka ci kyautar maratayin Zinari a wasannin Bolivarian da aka buga a shekarar alif 2005. Sai kuma wasanin Central America da Caribbean a shekarar alif 2006.

Wasan farko da ya buga a matsayin kwararren dan wasa, inda ya wakilci kasar tashi ta Kwalambiya inda suka fafata da kasar Uruguay. Mai tsaron ragar ya kafa tarihi na babu wani dan kwallo mai irin shekarunsa da ya wakilci kasar Kwalambiya sai shi mai tsaron ragar. Ya buga wasanni har guda 128 a kasar tashi, hakan yasa yafi duk wani dan wasa na Kwalambiya buga wasanni. Sunan dan wasan yazo a lamba ta farko a cikin jerin yan wasan da sukafi kowa buga wasanni a kasar Kwalambiya. Dan wasan ya wakilci kasar tashi a gasar kofin Copa America a shekaru mabanbanta har sau hudu sai kuma gasar cin kofin duniya har sau biyu.

Rayuwar Gida

gyara sashe

Ospina ya kasance siriki ne fa dan wasan ƙwallon ƙafa na kasar Kwalambiya wato James Rodriguez inda ya aurar da kanwar tashi wato Daniella ga dan wasan tsakiyar a shekarar alift 2011.[62] Sai dai kuma sun sanar da rabuwar tasu a shekara ta alif 2017.[63] Ospina ya auri mata yar asalin Kwalambiya mai suna Jesica Sterling tun shekarar alif 2012, sun haifi yarinya guda 1 sukay sa mata suna Dulce Maria sai kuma namiji daya mai suna Maximmiliano.[64][65]

Dan wasan, ya samu damar zama dan kasa a kasar Faransa saboda dadewa a cikin kasar. Ya samu wannan damar ne a shekarar alif 2014.[66]

Atlético Nacional

  • Categoría Primera A: 2005 Apertura, 2007 Apertura, 2007 Finalización

Arsenal

  • FA Cup: 2014–15, 2016–17
  • FA Community Shield: 2017

Napoli

  • Coppa Italia: 2019–20

Colombia U20

  • Central American and Caribbean Games: 2006

Colombia

  • Copa América third place: 2016, 2021

Individual

  • Saudi Pro League Goalkeeper of the Month: October 2022, April 2024

Manazarta

gyara sashe
  1. https://en.wikipedia.org/wiki/David_Ospina