Daoud Abdel Sayed ( Larabci: داود عبدالسيد‎ ) darekta ne kuma marubucin fim na Masar. An haife shi a birnin Alkahira a shekara ta 1946. Ya fara ne a matsayin mataimakin Youssef Chahine a The Land. Ya yi fina-finai da yawa da aka yabawawa.[1], kuma ya sami lambobin yabo na duniya da yawa musamman don shirin sa na The Land of Fear wanda aka yi a cikin 1999.

Daoud Abdel Sayed
Rayuwa
Haihuwa Kairo, 23 Nuwamba, 1946 (77 shekaru)
ƙasa Misra
Harshen uwa Egyptian Arabic (en) Fassara
Karatu
Harsuna Larabci
Egyptian Arabic (en) Fassara
Sana'a
Sana'a darakta, marubin wasannin kwaykwayo da marubuci
IMDb nm0008150
Daoud Abdel Sayed
Daoud Abdel Sayed

Rayuwar farko

gyara sashe
 
Daoud Abdel Sayed

An haife shi a cikin dangin 'yan Koftik a Alkahira, Abd El-Sayed ya kammala karatunsa a 1967 daga Cibiyar Fina-Finai mafi girma a Alkahira a matsayin darektan fim.[2] Daoud Abdel Sayed ya fara aikinsa a matsayin mataimakin darakta a muhimman fina-finai kamar " Al Ard " na Youssef Chahine, "Al Ragol Al Lazy Faqad Zaloh" na Kamal El Sheikh da "Awham El Hob". Duk da haka, ya gano cewa aikin mataimakin darakta ba nasa ba ne domin yana da babban buri kamar shirya fina-finai da samar da fina-finansa: “Wannan aikin ba nawa ba ne domin yana buƙatar a mai da hankali sosai, aabin da ba ni da shi. ".

Fina-finai

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe
  1. [1] Archived Oktoba 20, 2007, at the Wayback Machine
  2. Ten Arab filmmakers : political dissent and social critique. Gugler, Josef. Bloomington. 2015-06-29. p. 124. ISBN 9780253016584. OCLC 908447737.CS1 maint: others (link)

Karin Karatu

gyara sashe
  • Viola Shafik, "Daoud Abd El-Sayed: Parody and Borderline Existence" in: Josef Gugler (ed.), Ten Arab Filmmakers: Political Dissent and Social Critique, Indiana University Press, 2015, 08033994793.ABA, pp. 122–141

Hanyoyin Hadi na waje

gyara sashe