Dango Aboubacar Faissal Ouattara (an haife shi a ranar 11 ga watan Fabrairu shekarar 2002) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Burkinabé wanda ke taka leda a matsayin mai gaba ga Lorient.[1]

Dango Ouattara
Rayuwa
Cikakken suna Dango Aboubacar Faissal Ouattara
Haihuwa Ouagadougou, 11 ga Faburairu, 2002 (22 shekaru)
ƙasa Burkina Faso
Harshen uwa Faransanci
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
AFC Bournemouth (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
wing half (en) Fassara
Tsayi 1.77 m
Dango Ouattara

Aikin kulob/ƙungiya

gyara sashe

Samfurin matasa na kungiyar Burkinabe Majestic FC, Ouattara ya shiga 'yan sahun jira na kulob ɗin FC Lorient a cikin shekarar 2020. Ya sanya hannu kan kwantiraginsa na ƙwararru na farko tare da ƙungiyar a ranar 20 ga watan Mayu shekarar 2021. Ya fara wasansa na farko tare da Lorient a wasan 1 – 1 Ligue 1 da Saint-Étienne ranar 8 ga watan Augusta shekarar 2021.[2]

Ayyukan kasa

gyara sashe

Ouattara ya fara buga wasa na farko tare da tawagar kasar Burkina Faso a wasan sada zumunci da suka tashi 0-0 da Mauritania a ranar 30 ga watan Disamba shekarar 2021.

Ya zura kwallonsa ta farko a Burkina Faso a gasar cin kofin Afrika ta shekara ta 2021 da suka doke Tunisia.[3]

Jerin kwallayen da Dango Ouattara ya zura a raga
A'a. Kwanan wata Wuri Abokin hamayya Ci Sakamako Gasa
1 29 ga Janairu, 2022 Roumdé Adjia Stadium, Garoua, Kamaru </img> Tunisiya 1-0 1-0 2021 Gasar Cin Kofin Afirka

Manazarta

gyara sashe
  1. Dango Ouattara signe son premier contrat professionnel". FC Lorient. 20 May 2021.
  2. Saint-Etienne vs. Lorient - 8 August 2021-Soccerway". int.soccerway.com
  3. Strack-Zimmermann, Benjamin. "Mauritania vs. Burkina Faso (0:0)" . National Football Teams

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe
  • Dango Ouattara at Soccerway
  • Dango Ouattara at FootballDatabase.eu
  • Dango Ouattara at Global Sports Archive